‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Wajen Biki A Kaduna, Sun Kashe Mutane 13

[ad_1]

Ana zargin ‘yan bindiga sun kai hari wajen wani biki a ƙauyen Kahir da ke ƙaramar hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, inda suka kashe aƙalla mutane 13 tare da sace wasu.

Maharan sun kai harin ne da daddare ranar Lahadi, inda suka fara harbe-harbe a wajen bikin, lamarin da ya jefa mutane cikin firgici.

  • Taɓarɓarewar Sabis: NCC Ta Umarci Kamfanonin Sadarwa Su Biya Diyya
  • 2027: Ministocin Da Ake Tsammanin Za Su Yi Murabus Kafin Wa’adin Tinubu Na Ranar 31 ga Maris

Shaidu sun ce maharan, waɗanda ke ɗauke da manyan makamai, sun yi kusan awa ɗaya suna cin karensu ba babbaka ba tare da wani ya dakatar da su ba.

Wani mazaunin yankin, Shehu Bala, ya ce ‘yan bindigar sun isa wajen da misalin ƙarfe 11:47 na dare sannan suka fara harbi.

Ya ƙara da cewa wasu mutane biyu da ya sani sun ji rauni sakamakon harin.

An garzaya da waɗanda suka ji rauni zuwa Asibitin Kagarko, yayin da aka tura waɗanda suka fi muni zuwa manyan asibitoci a Kaduna domin samun kulawa ta musamman.

Wani jagoran al’umma ya tabbatar da cewa mutane 13 sun mutu kuma an riga an binne su.

Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin gano adadin mutanen da aka sace.

Haka kuma, maharan sun wawashe shaguna a yankin, inda suka kwashe kayan abinci, kayayyaki da magunguna daga wani shagon sayar da magani.

Mutane da dama sun tsere zuwa dazuka domin tsira da rayukansu.

‘Yansanda sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce suna ci gaba da bincike, ciki har da gano yawan mutanen da aka sace.

Sun kuma ce za su fitar da cikakken bayani bayan sun kammala bincike.

A halin yanzu, Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta ziyarci waɗanda suka jikkata a asibiti.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *