Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi
[ad_1]
Dubban mutane sun taru a Jihar Bauchi, don halartar jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa.
Gwamnatin Jihar Bauchi, ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu domin ba jama’a damar halartar jana’izar malamin.
Ɗalibansa da sauran Musulmi daga Bauchi da maƙwabtan jihohi sun isa da wuri domin halartar jana’izar.
Huumomi sun tsaurara matakai a jihar don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali.
Maulud Dahiru Bauchi, wanda ya yi magana a madadin iyalan marigayin, ya ce za a yi jana’izar malamin da misalin ƙarfe 3 na rana bisa wasiyyar malamin.
Ya ƙara da cewa Sheikh Sharif Saleh ne zai jagoranci jana’izar.
Jama’a da dama sun halarta, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, gwamnoni, sarakuna, ’yan kasuwa, attajirai da sauransu.
Iyalan mamacin sun ce dandazon mutanen da suka halarci jana’izar, ya nuna tasirin da Sheikh Dahiru ya yi wajen yaɗa addini da tarbiyya tsawon rayuwarsa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link