Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Koriya Ta Kudu
[ad_1]
Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta yi hira da Kim Hea Kyung, uwargidan shugaban kasar Koriya ta Kudu Lee Jae Myung, a birnin Beijing yau Litinin.
Peng ta yi maraba da Kim, wadda ta raka shugaba Lee a ziyararsa ta farko zuwa kasar Sin a farkon sabuwar shekara.
Da take bayyana cewa mabudin dangantaka a tsakanin kasa da kasa ya ta’allaka ne da zumunci na kusa a tsakanin mutane, Peng ta yi fatan cewa mutanen kasar Sin da Koriya ta Kudu a matsayin makwabta na kusa, za su kara fahimtar juna ta hanyar gudanar da cudanya a-kai-a-kai. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link