Gwamnatin Kano Ta Bai Wa Masu Son Yin Takara Wa’adin Yin Murabus Daga Muƙamansu

[ad_1]

Gwamnatin Jihar Kano ta umarci dukkanin jami’an gwamnati da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027 da su yi murabus daga muƙamansu kafin ranar 31 ga watan Maris, 2026.

Wannan umarni na ƙunshe ne cikin wata takarda da Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Farouk Ibrahim, ya fitar, wadda aka aike ga manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da kwamishinoni, masu ba da shawara, daraktoci da sauran masu rike da mukamai.

  • Yaki Bai Dace Da Moriyar Kowane Bangare Ba
  • Hisbah Ta Kano Ta Kama Matasa 583 Bisa Zargin Rashin Ɗa’a A Lokacin Sallah

Takardar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne bisa tanadin dokar zaɓe ta 2026, musamman sashe na 88(1), wanda ya haramta wa jami’an gwamnati shiga harkokin siyasa yayin da suke kan aiki.

Gwamnatin ta ce duk wanda ke son tsayawa takara dole ne ya yi murabus ko ritaya kafin wa’adin da aka ƙayyade, domin tabbatar da gaskiya, adalci da kuma kaucewa son rai a aikin gwamnati.

Haka kuma, an buƙaci a yaɗa sanarwar domin kowa ya sani kuma ya bi doka.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *