An Yi Liyafar Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin A Ofishin Jakadancin Sin Dake Togo

[ad_1]

A ranar 2 ga wannan wata, an yi liyafar murnar bikin bazara bisa kalandar gargajiyar Sinawa kuma bikin farko na birnin Lome na shekarar mu’amalar al’adu a tsakanin Sin da Afirka a ofishin jakadancin Sin dake kasar Togo, inda jami’an gwamnati da wakilan bangarori daban daban na kasar Togo, da jakadun kasa da kasa dake kasar Togo, da wakilan hukumomin jarin kasar Sin da kungiyoyin Sinawa dake kasar da yawansu ya zarce 500 suka halarci liyafar don murnar bikin bazara na kasar Sin.

A gun liyafar, an nuna bidiyon gabatarwar shirye-shiryen bikin bazara na kasar Sin na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG na shekarar 2026, mahalartar liyafar daga kasar Togo sun bayyana cewa, shirye-shiryen CMG sun burge su sosai, wadanda za su kasance dandalin sa kaimi ga jama’ar Afirka ciki har da ta kasar Togo wajen fahimtar al’adu da nasarorin bunkasar kasar Sin baki daya.

Ban da wannan kuma, an nuna bidiyon gabatarwar shirye-shiryen bikin bazara na kasar Sin na CMG na shekarar 2026 a liyafar murnar bikin bazara na kasar Sin da aka yi a ofisoshin jakadancin Sin dake kasashen Morocco da Isra’ila da Nicaragua da Argentina, da tsarin sufurin al’ummar biranen kasar Jamus, da kuma biranen Berlin da Stuttgart da Munich na kasar Jamus baki daya.

Hakazalika, an nuna bidiyon gabatarwar shirye-shiryen bikin bazara na kasar Sin na CMG na shekarar 2026 a taron murnar bikin bazara na shekarar 2026 a ofishin jakadancin Sin dake Myanmar, inda firaministan kasar Myanmar U Nyo Saw ya ziyarci wurin adana kayayyakin dake da nasaba da shirye-shiryen bikin na CMG da ganin al’adun bikin da kuma kayayyakin dake da nasaba da bikin baki daya. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *