Kuskure Ne Daukar Harkar Fim A Matsayin Sana’a Kadai —Maryam CTV (2)

[ad_1]

Bayan fim kina wata sana’ar ne?

Ina siyar da kayayyaki, su atamfofi, shaddodi, takalma, jakunkuna, kayan yara, sabulai masu hadi masu kyau da gyara jiki, ba wanda za su saka fari ko su lalata fuska ba.

Ko akwai wasu matsaloli a cikin masana’antar Kannywood wadanda ki ke ganin ya kamata a gyara su?

Ai matsaloli ba a cikin harkar fim ba, a zamanin nan na yanzu ko’ina akwai matsaloli. Alhmdulillahi mu yanzu mun samu shugabanni na kirki, wadanda suke ruke da ragamar wannan masana’antar me albarka wato Kannywood. Kamar irinsu; Abba El-Mustapha, mutum ne wanda ya san aikinsa ya san makaman aiki, kuma Alhamdulillahi idan da abubuwa duk sun babbaci, yanzu Alhamdulillahi komai ya fara gyaruwa. Yaushe rabon a ji an ce wani dan fim ko ‘yar fim ta janyo magana ko ta dauko wani abu, babu wannan. Sai kuma abin da zan fada ya kamata ace mu iyaye mata ko maza ana girmama mu sosai fiye ma da yadda ake yi mana a baya. Tunda mu gaskiya mun dade muna gwagwarmaya a harkar nan, in ritaya ne ma ai yanzu ana maganar mutum ya kusa ritaya. Duk da in ka yi ritayar ba fansho za a baka ba, ya danganta da yadda furodusa ya dauke ka, amma ni ina kira ne ga furodusoshin tunda su daraktoci saka su ake su yi a biya su. Amma furodusa shi ne dungurugun me aiki a hannu, me kuma kudi a hannu. Ya rika tausayawa ‘yan tsofaffin nan da suka dade a cikin Kannywood, shi ne kawai abin da zan kira.

Misali ki zama shugaba, wane irin cigaba ki ke ganin za ki kawo ga masana’antar Kannywood?

Ni ina ni ina shugabanci, ai shugabanci ya danganta da yadda mutum yayi karatunsa ko gwagwarmayarsa, ba wai na ce ba zan iya shugabanci ba a’a, yanzu muna da zakakuran shugabanni wanda suka tsaya akan harkar. Daman in ka ji ana ina ma ni ne nake shugabanci to, abu ya kwabe an rasa me gyara, amma yanzu Alhmdulillah komai ya gyaru.

Wadanne irin tambayoyi aka fi yi miki da zarar an ci karo da ke a zahiri?

Bai wuce na fim ba, irin na ganki a kaza ya aka yi ki ka yi kaza da sauransu, ko su yi min tambayoyi akan abokan sana’a ta, ko su ce na basu lambar wata abokiyar sana’a ta. Gaisuwa dai na mutunci da darajantawa.

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shigowa cikin masana’antar Kannywood?

Farko su fara da gida, a nemi shawararsu da yardar su. Dan duk abin da iyayenka suka yarda suka baka shawara a kai da amincewarsu duk inda ka shiga, in Allah ya yarda za ka samu nasara. In babu iyaye a nemi shawarar ‘yan’uwa wanda suka isa da su. Idan sun shigo su bi shugabanni su bigirmama su, mu ma iyayensu da akwai kakanninsu ma su gurmamasu. Wacce ta fi ka ta zama Antinka da can haka ake a Kannywood. Sannan kar ki ga kin samu damar fara fim ki je ki ta zuba iyashege, ko a rika ganinki wuraren da bai dace ba, in an kama ki ki ce ke ‘yar fim ce. To, wannan ba daidai ba ne.

Ko akwai wata shawara da za ki bawa sauran abokan sana’arki na fim?

Alhmdulillahi mu mata kanmu a hade yake, muna zaune lafiya muna mutunta juna, muna ganin girman juna  in wani abu ya tashi na wani za mu dunguma mu je, in na jaje ne mu jajanta masa, in na farinciki ne mu nuna farincikinmu. Daga bangaren mu manya mata kenan.

Me za ki ce da gidan jaridar LEADERSHIP HAUSA, har ma da masu karanta wannan hirar taki?

Sai dai na ce Allah ya kara daukaka, gaskiya kuna fitowa al’umma da manufofi da bayanai akan duk wanda ya kamata su sani, masu karatu idan kuna so ku ji tarihi gaskiya to, ku nemi Jaridar LEADERSHIP HAUSA za ku ji cikakken labarin mutum, kuma daman an ce Waka a bakin me ita ta fi dadi. Allah ya kara muku basira ya kara daukaka, na gode sosai.masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood. A wannan makon mun kawo muku ci gaban hirar da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta yi da fitacciyar jarumar wacce ta shafe sama da shekaru ashirin a cikin masana’antar Kannywood wato, HAJIYA MARYAM SULAIMAN wacce aka fi sani da MARYAM CTB. Inda ta bayyanawa masu karatu babban cigaban da masa’antar Kannywood ta samu a yanzu, da kuma wasu abubuwa da masana’antar ta rasa a yanzu sabanin shekarun baya. Baya ga haka jarumar ta yi kira ga furodusas kan wani nauyi da ya kamata su sauke shi, hadi da wasu batutuwa masu yawan gaske da suka shafi masana’antar da kuma masu yunkurin shiga cikin masana’antar, har ma da wasu batutuwan masu yawa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *