DSS ta tsare jami’inta da ake zargi da auren yarinya ƙarama

[ad_1]



Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), ta bayyana cewa ta tsare ɗaga daga cikin jami’anta da ake zargi da sace wata yarinya ’yar shekara 16, wadda ya tilasta wa sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci.

Wata kotun majistare da ke zamanta a garin Hadejia na Jihar Jigawa, ta bayar da umarnin kama tare da binciken jami’in DSS bisa zargin tsare yarinyar.

Wannan umarni ya biyo bayan ƙorafi da wasu lauyoyi ƙarƙashin Gamji Lawchain suka shigar.

Lauyoyin suna wakiltar mahaifin yarinyar mai suna Walida Ibrahim.

Lauyoyin sun ce jami’in DSS ɗin ya sace Walida sama da shekaru biyu da suka wuce.

Sun zarge shi da tsare ta ba bisa ƙa’ida ba, cin zarafinta ta hanyar saduwa da ita, da kuma tilasta mata sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci ba tare da izinin iyayenta ba.

Sun kuma ce ta haihu biyo bayan ciki da ya yi mata.

Lauyoyin sun yi Allah-wadai da abin da suka kira amfani da iko ta hanyar da ba ta dace ba.

Sun buƙaci a dakatar da jami’in nan take, a kama shi, a gurfanar da shi gaban kotu, tare da gudanar da bincike a kansa.

Sun ce lamarin ya jefa iyalan Walida cikin damuwa da tashin hankali.

Lauyoyin sun ce lamarin baƙin ciki da iyayen yarinyar suka shiga ya yi sanadin mutuwar mahaifiyarta.

Hukumar DSS ta mayar da martani, ta hanyar fitar da wata sanarwa a ranar 9 ga watan Janairu, 2026.

Sanarwar ta fito daga bakin Favour Dozie, Mataimakiyar Darakta da Hulɗa da Jama’a da Sadarwa ta DSS a Babban Ofishin na Ƙasa.

Ta ce su a gudanar da bincike kan lamarin kuma za su sanar da jama’a sakamakon binciken.

Ta kuma bayyana cewa ba daidai ba ne bayyana sunan jami’in ba.

“Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta samu labarin wani rahoto da ake zargin wani jami’inta mai suna Ifeanyi Festus da hannu a sata, lalata da ƙaramar yarinya, da kuma amfani da muƙaminsa ba bisa ƙa’ida.

“Domin fayyace gaskiya, hukumar ba ta da wani ma’aikaci mai wannan suna a cikin jerin ma’aikatanta.”

“Amma, muna tabbatar da kama wani jami’in DSS, mai suna Ifeanyi Onyewuenyi, wanda ake zargi da tilasta wa wata yarinya mai suna Walida Abdulhadi, sauya addininta tare da aurenta, ana bincike a kansa.”

“Irin waɗannan ayyuka sun saɓa wa dokokinmu da ƙa’idar aiki. Don haka, za a sanar da jama’a sakamakon binciken a nan gaba.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *