Hukumar Kwastam Ta Fitar Da Wasu Sabbin Ƙa’idoji Ga Kamfanonin Rabar Da Kaya

[ad_1]

Hukumar Kwastam ta Ƙasa ta fitar da wasu sabbin ƙa’idoji gudanar a ayyukan rabar da kaya da a turance, ake kira da   SOP.

Kwastam ta  ɗauki wannan matakin ne, bisa nufin saita gudanar da ayyukansu da kuma ƙara bunƙasa hada-hadarsu, ta kai kayan.

Kazalika, Hukumar ta Kwastam, ta samar da wannan sabbin ƙa’idojin ne, domin kamnfanunin su rinƙa bin ƙa’idojin da Hukumar ta shinfiɗa da kuma rage yawan jinkirin da kamfanonin ke fuskanta, wajen kai kayan ga masu su da kuma kaucewa, aukuwar duk wata ta’addama.

  • Kotu Ta Yi Wa Wani Mutum Bulala, Ta Tura Shi Makarantar Islamiyya A Kano
  • Shirin Sauya Sheƙa: An Tsaurara Tsaro A Harabar Gidan Gwamnatin Kano

Kamfnonin da ke gudanar da ayyukansu na kai kayan a ƙarƙashin tsarin biyan kuɗin kai kaya wato DDP, na buƙatar kamfanonin, su bi waɗannan sabbin ƙa’idojin ciki har da takardun kundi da takardun da kamfanonin, suka biya harajinsu.

Wanzar da waɗannan sabbin ƙa’idojin dai, ana sa ran za su ƙara haɓaka ayyukan kamfanonin da kuma tatatra da cewa, ana bin ƙa’idoj da kuma rage kamfanonin nauyin.

Kazalika, hakan zai kuma taimaka wa Hukumar ta Kwastam, damar sanya ido kan ayyukan da kamfanonin suke gudanawar tare da kuma tabbatar da cewa, suna kiyaye dokokin Hukumar ta Kwastam.

Mataimakin Kwantirola a Hukumar ta Kwastam Dakta Abdullahi Maiwada, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin da ta gabata ya bayyana cewa, wanzar da waɗannan sabbin ƙa’idojin, za su samar da daidaito, wajen yiwa kamfnonin rijista da tabbatar da suna bin ƙa’ida da kuma samun damar sanya ido, kan ayyukan da suke gudanarwa, waɗanda za su kasance, sun yi daidai da na faɗin duniya.

Maiwada ya ƙara da cewa, shirin  na DDP, ya samo asali ne, da yarjejeniyar ƙungiyar baje koli ta ƙasa da ƙasa wato  ICC, tun a  2020, wanda Hukumar ta Kwastam ke yin amfani da wani ɓangare na wannan yarjejeniyar, bisa doka ta 2023, da ke buƙatar ganin an gudanar da hada-hadar kasuwanci, ba tare da wata matsala ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *