Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kammala Karɓar Filin Wasa Na Ahmadu Bello
[ad_1]
Filin wasa na Ahmadu Bello Stadium da ke Kaduna na shirin samun gagarumin sauyi bayan sanya hannu kan yarjejeniyar mayar da mallakinsa ga Gwamnatin Jihar Kaduna a ranar 26 ga Fabrairun 2026.
Gyara da kula da filin mai ɗumbin tarihi yanzu za su koma hannun gwamnatin jihar, bayan da shugaban National Sports Commission (NSC), Shehu Dikko, da gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a hedikwatar NSC da ke Abuja.
- Masu Safarar Makamai Sun Faɗa Komar Ƴansanda A Kaduna
- Ramadan: Coci Ta Raba Kayan Abinci Ga Makarantun Tsangaya A Kaduna
Wannan mataki ya biyo bayan amincewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ba da damar fara aikin gyaran filin.
Daga cikin ayyukan da za a gudanar akwai sabunta ciyawar tsakiyar fili da kuma faɗaɗa kujerun zama daga 12,000 zuwa 32,000. Ana sa ran gyaran zai mayar da Kaduna cibiyar wasanni da yawon buɗe ido a Nijeriya.
[ad_2]
Source link