An kama ɗan China kan zargin yi wa mace fyade a wajen fasa dutse

[ad_1]



An kama wani ɗan ƙasar China mai shekaru 59 bisa zargin yi wa wata mata fyade a wani wajen fasa dutse da ke yankin Kobape a jihar Ogun.

Aminiya ta ganbo cewa lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Janairu, 2026, a wurin fasa dutsen da ke yankin.

Wani babban jami’in tsaro, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da ’yan jarida, ya ce an kama wanda ake zargi bayan korafi daga wacce aka yi wa fyaden.

“An kama wani ɗan ƙasar China mai shekara 59 bisa zargin yi wa mace fyade a wurin hakar dutse da ke Kobape,” in ji majiyar.

“An gaggauta tsare wanda ake zargi, kuma an mika shari’arsa ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun da ke Eleweran domin gudanar da cikakken bincike.”

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Ogun, Babaseyi Oluseyi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rundunar ta fara cikakken bincike kan zargin.

“Bincike yana ci gaba da gudana,” in ji Oluseyi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *