INEC ta sanar da ranar zaben kananan hukumomi a Abuja
[ad_1]
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa zaɓen ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya (FCT) zai gudana a ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairu, 2026.
Hakan na zuwa ne yayin da hukumar ta sanar da yi wa sabbin jam’iyyu guda biyu rajista a shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin taron farko na tattaunawa da jam’iyyun siyasa tun bayan da ya hau kujerar shugabancin hukumar.
Amupitan ya ce zaɓen na Abuja zai shafi masu kada kuri’a 1,680,315 da aka yi wa rijista a rumfunan zaɓe 2,822 da ke cikin ƙananan hukumomi shida.
Kananan hukumomin sun hada da Abaji, AMAC, Bwari, Gwagwalada, Kuje da Kwali.
“Zaɓen zai gudana ne tsakanin ’yan takara 570 a mazabu 68 domin kujerun Ciyaman, mataimakin Ciyaman da kuma Kansiloli,” in ji shi.
Ya cewa hukumar ta kammala yawancin shirye-shiryen da suka haɗa da raba kayan zaɓe marasa matsala, horas da ma’aikatan zaɓe, ɗaukar ma’aikatan wucin gadi da kuma saita na’urorin BVAS domin tantance masu kada kuri’a da tura sakamakon zabe zuwa shafin duba sakamakon zabe na INEC (IReV).
“Domin tabbatar da ingancin tsarinmu, hukumar za ta gudanar da gwajin tantance masu kada kuri’a a ranar Asabar, 7 ga watan Fabrairu, 2026, a rumfunan zaɓe 289 da aka ware a cikin ƙananan hukumomi, shida,” in ji Amupitan.
Shugaban na INEC ya gargadi jam’iyyun siyasa kan sayen kuri’a, yana mai bayyana hakan a matsayin “lalata manufar dimokuraɗiyya da kuma karya doka,” inda ya ce masu laifin za su fuskanci hukunci.
Kan rajistar sabbin jam’iyyun kuwa, Amupitan ya sanar da cewa hukumar ta yi wa jam’iyyun DLA da NDC rajista bayan sun cika dukkan sharuddan da kundin tsarin mulki da na doka suka gindaya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link