Daga Karshe Tawagar Super Eagles Ta Sauka A Uyo Bayan Saukar Gaggawa A Angola

[ad_1]


Tawagar Super Eagles ta Nijeriya sun isa birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, bayan da wata tangarɗa ta janyo jirginsu ya yi saukar gaggawa a kasar Angola bayan buga wasan zagaye na 9 na gasar neman gurbin buga gasar Kofin Duniya a kasar Afirka ta kudu ranar Asabar.

Tawagar Super Eagles ta sauka lafiya a filin tashi da saukar jiragen sama na Victor Attah dake Uyo da misalin karfe 8:05 na safiyar yau, tawagar ta Nijeriya dai na kan hanyarta ne daga Polokwane na kasar Afirka ta Kudu zuwa birnin Uyo lokacin da jirginsu ya hadu da bugun gilashi bayan tashinsa daga birnin Luanda na kasar Angola, inda ya tsaya ya sha mai.

Rahotanni sun bayyana cewa, matukin jirgin ya ci gaba da gudanar da ayyukansa a lokacin da lamarin ya faru kuma ya sarrafa jirgin cikin fasaha zuwa filin jirgin sama na Luanda, tare da tabbatar da tsaron duk wanda ke cikin jirgin, zuwa yanzu dai ba a samu wani rahoton rauni ba.

Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) ta tabbatar da cewa ta dauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin inda aka aike da wani jirgin sama daga Legas domin jigilar tawagar zuwa Uyo, sai dai lamarin ya haifar da tsaiko a shirin da tawagar ta ke yi na tunkarar jamhuriyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *