Ministan Wajen Nijeriya Ya Fitar Da Mukalar Taya Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Huldar Diplomasiyya Tsakanin Nijeriya Da Sin
[ad_1]
Ministan harkokin wajen kasar Nijeriya Yusuf Maitama Tuggar ya fitar da mukala mai taken “Cika shekaru 55 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Nijeriya da Sin: Huldar abota ta samu ci gaba tare cikin sabon zamani”, ranar Talata a shafin jaridar China Daily, don taya murnar cika shekaru 55 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.
A mukalarsa, ministan ya ce, tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, sun yi ta martaba juna da cin moriyar juna, tare da bunkasa huldar kasashensu da ma inganta hadin gwiwarsu yadda ya kamata. A watan Satumban shekarar 2024, kasashen biyu sun daukaka huldarsu zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. Lamarin da ya shaida niyyarsu ta hada hannu da juna wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakaninsu. Bunkasar huldar kasashen biyu ba bayyana burin bai daya na al’ummunsu kadai ya yi ba, har da nuna yadda kasashe masu tasowa ke dada habaka tasirinsu a duniya, wanda hakan ke da ma’ana mai muhimmanci. Ya ce, Nijeriya ta yi imanin cewa, inganta hadin gwiwarta da kasar Sin muhimmiyar dama ce ta tabbatar da dauwamammen ci gaba da ci gaban juna, kuma hakan zai samar da karin tabbas da karfi ga duniyar da ke fama da tashe-tashen hankula.
A wannan rana kuma, cibiyar nazarin harkokin kasar Sin da cibiyar nazarin harkokin zaman lafiya da daidaita rikici na Nijeriya sun shirya taron tattaunawa mai jigon “Waiwaye adon tafiya: Cika shekaru 55 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Nijeriya da Sin”, kuma mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da darektan sashen kula da harkokin yankin Asiya da Pasifik na ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya da ma sauran mutane sama da 100 da suka fito daga bangarori daban daban na Nijeriya sun halarci taron.
Mukaddashin jakadan kasar Sin a Nijeriya, Zhou Hongyou shi ma an ba shi goron gayyata, inda ya gabatar da jawabi a wajen taron. A jawabinsa, ya ce, ran 10 ga watan Faburairu rana ce ta cika shekaru 55 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Nijeriya, kuma ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun aika wa juna sakwannin taya murna, inda suka sake tabbatar da niyyarsu ta kara bunkasa huldar kasashen biyu cikin sabon zamani bisa daidaiton da shugabanninsu suka cimma. (Lubabatu Lei)
[ad_2]
Source link