El-Rufai Zai Amsa Goron Gayyatar EFCC A Ranar Litinin — Lauyansa

[ad_1]

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zai amsa goron gayyatar da Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Litinin.

Lauyansa, Ubong Esop Akpan ne, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake mayar da martani kan rahotanni cewa jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin kama El-Rufai a Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

  • Gwamnatin Kano Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Hana Kwankwaso Shigowa Kano — Buba Galadima
  • Jami’an Tsaro Sun Ƙwace Fasfon El-Rufai A Filin Jirgin Saman Abuja – Hadimi

A cewar lauyan, jami’an tsaro sun tunkari El-Rufai ne da yammacin ranar Alhamis bayan ya dawo daga birnin Alkahira na ƙasar Masar, a cikin jirgin EgyptAir.

Mista Akpan ya ce EFCC ta aike da wasiƙar gayyata zuwa gidan El-Rufai lokacin da yake ƙasar waje, don haka ba zai yiwu ya amsa gayyatar nan take ba.

Ya ƙara da cewa tun a watan Disamban 2025 suka sanar da EFCC cewa El-Rufai zai samu damar zuwa hukumar sai ya dawo Najeriya.

Ya ce sun bayyana a fili cewa zai je ofishin EFCC da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026.

Lauyan ya ce duk wani yunƙurin kama shi duk da ya amince zai je da kansa, bai dace ba kuma ya saɓa wa tsarin doka.

Haka kuma ya buƙaci a dawo masa da fasfo ɗinsa, wanda ya ce an karɓe shi a lokacin da lamarin ya faru a filin jirgin saman Abuja.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, EFCC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan batun ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *