INEC ta gabatar da kasafin N873.78bn don zaɓen 2027

[ad_1]



Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta gabatar da kasafin Naira biliyan 873.78 don gudanar da zaɓukan shekarar 2027, tare da kaso mai tsoka ga ayyukan zabe, amfani da na’urar fasaha da kuma kuɗaɗen da za a kashe wajen kayayyakin.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana hakan a gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Majalisar Wakilai kan harkokin zaɓe a zauren majalisar a ranar Alhamis.

Shugaban na INEC ya bayyana cewa, an shirya kasafin ne daidai da sashe na 3(3) na dokar zaɓe ta 2022, wanda ya wajabta wa hukumar ta shirya kasafin kuɗin zaɓen ta aƙalla shekara guda kafin babban zaɓe.

Ya ce, ya zama dole a ware kasafin da wuri domin tabbatar da isassun tsare-tsare da kuma aiwatar da zaɓukan ƙasar baki ɗaya ba tare da wata matsala ba.

Daga taƙaitattun shawarwarin, hukumar ta raba kasafin zuwa manyan sassa huɗu.

Ayyukan zaɓe sun kasance kaso mafi tsoka da ya kai Naira biliyan 375.75, wanda ya shafi ayyukan da suka shafi gudanar da zaɓen kai tsaye.

An yi hasashen kashe kuɗaɗen gudanar da zaɓe a kan Naira biliyan 92.31, yayin da farashin amfani da na’urar fasahar zaɓe ya kai Naira biliyan 209.21, wanda ke nuna yadda Hukumar ke ci gaba da dogaro da hanyoyin da ake amfani da su na fasaha.

INEC ta kuma bayar da shawarar Naira Biliyan 154.90 na kuɗaɗen da za a kashe a babban zaɓen.

A dunƙule kum,a, manyan abubuwa guda huɗu sun kai Naira biliyan 832.17. Amupitan ya bayyana cewa, an ware ƙarin Naira biliyan 41.61 don wasu kuɗaɗe daban-daban, wanda ya kawo jimillar ƙudirin kasafin kuɗin zaɓen 2027 zuwa Naira biliyan 873.78.

Amupitan ya yi nuni da cewa, babban abin da wannan ƙudiri ya bayar ya fi na kasafin kuɗin da ya gabata, yana mai bayanin cewa da yawa daga cikin manyan abubuwan da ba a ayyana su ba yadda ya kamata ba a cikin kudaden da aka ware a baya ba, yanzu an haɗa su cikin kasafin babban zaɓen 2027.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *