Tsaro: Har Yanzu ‘Yan Ta’adda Na Ci Gaba Da Yi Wa Mutane Kisan Kiyashi A Arewa
[ad_1]
Kusan shekaru 20 kenan ana fama da hare-haren ‘yan ta’adda, tun daga hare-haren mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas ya zuwa ga na ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya a Nijeriya.
Jihohin da Boko Haram/ISWAP suka fi addaba, su ne Borno, Yobe, da Adamawa inda ta’addancin ‘yan bindiga kuma yafi ƙamari, su ne kamar haka: Jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Neja, Kwara, Benuwe, Taraba da wasu sassan jihar Kano. Wadannan hare-hare sun jawo asarar rayuka, dukiyoyi, da kuma raba dubban mutane da matsugunansu.
- Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Hukumar Alhazai Ta Ƙasa Ambasada Ismail Abba Yusuf
- NNPP Ta Yi Watsi DA Rahoton Hukuncin Amurka Kan Kwankwaso
‘Yan bindigar na kai hare-hare ne ta hanyoyi daban-daban, ciki har da
Kai farmaki kauyuka da daddare ko da sanyin safiyar asuba, inda suke harbe-harbe kan mai-uwa-dawabi, domin sace mutane a basu kudin fansa, wani lokaci kuma domin sace dabbobi.
Wani lokaci kuma, su kan tare hanya, domin garkuwa da mutane, bayan sun kashe wasu.
Har ila yau, wani lokacin, haka nan, sai su kai hare-harensu ga makarantun firmware da sakandire na gwamnati, duk don neman kudin fansa.
Wadannan hare-haren, sun haifar da matsaloli masu yawa, tun daga asarar rayukan daruruwan mutane; dubban mutane, na rasa matsugunansu ta hanyar yin hijira domin tsira da rayukansu; Durkushewar noma da kasuwanci; Taɓarɓarewar ilimi, inda rufe makarantu saboda tsaro ya zama ruwan dare.
Masana na danganta karuwar matsalar tsaro da wasu dalilai kamar, Talauci da rashin aikin yi; Yawaitar makamai ba bisa ka’ida ba, Raunin tsarin tsaro a wasu yankuna, Rikice-rikicen makiyaya da manoma.
Matsalar ‘yan bindiga a Arewacin Nijeriya ta zama babbar barazana ga tsaro da ci gaban kasa. Don shawo kan wannan matsala, dole ne a hada kai tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro, shugabannin al’umma da kuma talakawa domin samar da dorewar zaman lafiya.
[ad_2]
Source link