Tun da Uba Sani ya hau mulki na fita batunsa — El-Rufai

[ad_1]



Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa bai taɓa ɗaukar kansa a matsayin ubangida ga Gwamna Uba Sani ba, kuma ba ya sha’awar irin wannan tsarin siyasa.

A yayin wata tattaunawa ta musamman da Trust TV ta yi da shi, El-Rufai ya ce ba shi da wata alaƙa ta musamman da Gwamna Uba Sani, bayan barinsa mulki.

Ya bayyana cewa tun kafin Zaɓen 2023 ya shaida wa Uba Sani cewa da zarar ya ci zaɓe, zai ba shi cikakkiyar dama ya yi mulki ba tare da ya tsoma masa baki ba.

“Na yi bayani a fili cewa da zarar mun tabbatar da nasararsa, zan miƙa mulki in tafi. Ban ma je Kaduna cikin watanni shida na farko ba, domin na ba shi sarari ya natsu. Ban taɓa kiran Uba Sani ba tun bayan bari na mulki. Shi ne zai kira ni idan yana buƙatar shawara,” in ji shi.

El-Rufai ya ce ba ya sha’awar kula da wanda ya gaje shi a kujerar mulki, kuma ba ya son zama mai iko a bayan fage.

Ya ƙara da cewa ba ya sha’awar tsarin siyasar ubangida da ake dangantawa da wasu jihohi kamar Legas da Kano.

Ya kuma kawo labarin da tsohon shugaban soja ya faɗa masa a lokacin yana mulki, inda ya bayyana yadda kujerar mulki ke sauya yanayi har ma tsakanin uba da ɗa.

“Wannan tsohon shugaban ya ce min, ko da ɗanka ne ya hau wannan kujera, rana ta farko zai gaishe ka da girmamawa. Amma rana ta uku, idan ba ka gaishe shi da mutunci ba, matsala za ta iya tasowa. Wannan shi ne abin da na koya tun ina matashi, cewa mulki abu ne mai ban mamaki,” in ji El-Rufai.

Ya ce tun daga lokacin ya zama mai adawa da tsarin siyasar ubangida, kuma ya yi magana a Legas kan batun, lamarin da ya jawo masa suka daga magoya bayan Tinubu.

Dangane da hulɗarsa da Uba Sani, El-Rufai ya ce ba ta taɓa rushewa ba, sai dai ba shi da alaƙa ta kai tsaye da shi.

“Ban ma tuna lokacin ƙarshe da ya kira ni ba. Wataƙila fiye da shekaru uku ke nan,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *