CGTN: Mafarkin Amurka Ya Lalace Zuwa Rudi Na Cin Zali

[ad_1]

Kimar Amurkawa masu ikirarin kare hakkin dan adam na zubewa sakamakon kundin bayanan Epstein da ake fitarwa. Wannan sumin tabi ne na irin laifukan da masu fada a ji na Amurka suka aikata, wanda ya bankado tarin kura kuran dake cikin baki dayan tsarin siyasa da zaman takewa da al’adun kasar. Batun ‘yanci da hakkin da adam da Amurka ke amfani da su wajen bayyana kanta da kafa hujjar yi wa kasashen waje katsalandan, ba za su taba rufe laifuffukanta na keta hakkin dan adam ba. Mafarkin Amurka ya lalace zuwa rudi na cin zali.

Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar ya nuna cewa, kaso 92 na masu bayar da amsa sun yi imanin cewa, batun na Epstein ya bankado yadda tubalin ka’ida ta bai daya na tsarin siyasar Amurka ya lalace baki daya, da yadda ba za a taba magance matsalar jari hujja ba a kasar.

An fitar da nazarin ne a dandamalin CGTN na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane masu amfani da intanet 9,690 suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Mai fassara: FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *