Tinubu Ya Yi Maraba Da ‘Yan Matan Makarantar Kebbi Da Aka Kuɓutar

[ad_1]


Shugaba Bola Tinubu ya yi maraba da sakin dalibai mata su 24 da ‘yan ta’adda suka sace a makarantar sakandire Maga, da ke karamar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi.

‘Yan ta’adda sun kai hari a makarantar ne da asubahin ranar Laraba, 17 ga Nuwamba, inda suka sace ‘yan matan, jim kaɗan bayan kwashe sojoji daga harabar makarantar.

Bayan sace ɗaliban na Kebbi, an kuma sace masu ibada a coci da ke Eruku a jihar Kwara da wasu ɗalibai kuma a Papiri a jihar Neja.

An saki dukkan wadanda aka sace a Eruku su 38 a ranar Lahadi. A wannan rana, shugaban kungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar Neja ya ce, 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da ‘yan bindiga suka sace a jihar Neja sun tsere daga hannun masu garkuwa da su.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro kan duk kokarin da suke yi don tabbatar da an kuɓutar da duk waɗanda ‘yan ta’addan suka sace.

Ya umurci jami’an tsaro da su ƙara ƙoƙari don ceto sauran ɗaliban da har yanzu ake tsare da su.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *