An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi

[ad_1]



Aƙalla makiyaya goma aka kashe a wani hari da aka kai wa Fulani makiyaya a wata ruga da ke yankin Tilli a ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar Kebbi.

Majiyarmu ta ce harin wanda ya yi kama da na ramuwar gayya na zuwa ne bayan kashe wani ɗan sa-kai a yankin.

Bayanai sun ce mutuwar ɗan sa-kan ce ta jawo zargin cewa Fulani ne suka yi kisan, lamarin da ya sa wasu matasa suka dunguma suka kai farmaki a sansanin Fulani, inda suka kashe mutum goma a yayin harin.

Wani mazaunin yankin da ya zanta da wakilinmu ya ce, “kuskuren fahimta ce ta sa aka kai harin.

“Sun ɗauka cewa Fulani ne suka kashe ɗan sa-kan, sai suka kai musu hari a sansaninsu.

“Mutum sama da goma aka kashe, har yanzu ma suna ci gaba da neman wasu da ba a gani ba.”

Majiyar ta ƙara da cewa, Shugaban Ƙasa na ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida, sun ziyarci yankin domin jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce bai samu labarin lamarin ba a lokacin, amma ya yi alƙawarin binciko gaskiyar abin da ya faru.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, bai waiwayi wakilinmu ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *