Ganduje Ya Koma Abuja Daga Landan, APC Na Shirye-shiryen Karɓar Gwamnan Kano
[ad_1]
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya isa Abuja da safiyar Lahadi, 26 ga Janairu, 2026, bayan dawowa daga birnin Landan. Majiyoyi sun ce ana sa ran zai wuce Kano domin halartar shirye-shiryen tarɓar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.
Gwamna Abba Yusuf, wanda ya samu nasara a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a hukumance a jiya Lahadi, tare da bayyana dalilin ficewarsa da rikicin shugabanci da shari’o’in kotu da suka dabaibaye jam’iyyar. Wannan mataki ya haifar da sabon yanayi a siyasar jihar Kano, inda ake sa ran zai koma APC.
- Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
- 2027: Ganduje Ya Gargaɗi Mambobin APC Kan Fara Tallata Masu Neman Takarar Gwamna Da Wuri
Majiyoyin jam’iyyar APC sun ce ana shirin tarɓar gwamnan tare da manyan shugabannin jam’iyyar a Kano, kuma ana sa ran Dr. Abdullahi Ganduje zai jagoranci taron karɓar sa, a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa APC a jihar.
A baya, Gwamna Abba Yusuf ya taɓa zama mamba a jam’iyyar APC kafin ya koma PDP, daga bisani kuma NNPP tare da ubangidansa ada Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya lashe zaɓen gwamna. Masu lura da al’amuran siyasa na ganin komawarsa APC na iya sauya ma’aunin siyasa a Kano da ma Arewa gaba ɗaya.
[ad_2]
Source link