An haramta bukukuwan aure a Taraba

[ad_1]



Ƙungiyar Musulmi ta Jihar Taraba, ta haramta dukkanin wasu bukukuwan da ake yi kafin a ɗaura aure, sai dai taron addu’ar ɗaurin aure, wanda Musulunci ya amince da ita.

Wannan doka ta haramta Ranar Ƙauyawa, wato bikin da ake yi gabanin ɗaura aure, inda matasa kan saka kaya da yin ado maras kan gado.

Haka kuma ta haramta ranar ‘mother’s day’ da taron Ajo, inda abokai da dangi ke tara wa ango gudunmawa.

Ƙungiyar ta bayyana cewa haramcin ya samu amincewar dukkanin limaman Jalingo, sarakuna da hukumomi.

A ranar Juma’a da ta gabata ne limaman masallatan Juma’a a Jalingo suka sanar wa jama’a wannan doka yayin huɗubarsu.

Imam Tajudeen Nuhu, limamin masallacin Juma’a na Tashar Mayo Gwoi, shi ne ya bayyana wannan umarni a madadin ƙungiyar Musulmi ta jihar.

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa duk Musulmin da ya karya wannan doka, ba wani malami ko liman da zai halarci gidansa domin halartar ɗaurin aure, raɗin suna ko kuma sallar jana’iza.

Haka kuma, an gargaɗi limamai cewa duk wanda ya amince ya jagoranci irin waɗannan abubuwa a wajen wanda ya karya dokar, za a hukunta shi tare da tsige shi daga limanci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *