Neman a kashe waɗanda suka hallaka uwa da ’ya’yanta a Kano ya saɓa da dokokin Najeriya — Lauya
[ad_1]
Wani lauya a Jihar Kano, Mubarak Abubakar, ya ce kiran da ake yi kan a gaggauta kashe waɗanda aka kama bisa zargin kashe wata uwa da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi-Chiranci, ba daidai ba ne kuma ya saɓa wa tsarin shari’ar laifuka na Najeriya.
Yayin da yake bayani daga mahangar shari’a, lauyan ya ce ba za a iya aiwatar da hukuncin kisa ga kowa ba sai kotu mai ikon yanke hukunci ta same shi da laifi.
Ya ce hakan zai tabbata ne, bayan wanda ake zargin ya gama amfani da dukkanin damar ɗaukaka ƙara da kundin tsarin mulki ya tanada.
“Ba za a iya kashe mutum ba sai an yi masa shari’a, an same shi da laifi, kuma kotu ta yanke masa hukunci,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ko bayan kotu ta yanke hukunci, doka ta bai wa wanda aka same shi da laifi damar ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗaukaka ƙara, sannan daga bisani zuwa Kotun Ƙoli.
“Kundin Tsarin Mulki ya tanadi wani lokaci da kowane wanda aka same shi da laifi zai iya ɗaukaka ƙara. Har sai an gama waɗannan matakai na shari’a, ba za a iya aiwatar da hukuncin kisa bisa ƙa’ida ba,” in ji Abubakar.
A cewarsa, sai bayan kotun ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe kuma babu sauran damar ɗaukaka ƙara ne, za a iya aiwatar da hukuncin kisa.
“Ba tare da kotu ta tabbatar da laifin mutum da kanta ba, kuma dukkanin matakan ɗaukaka ƙara sun ƙare, ba za a iya hanzarta wannan kisa da ake magana a kai ba,” kamar yadda ya ƙara faɗa.
Abubakar ya jaddada cewa duk da cewa ana iya samun tashin hankali a shari’o’in da suka shafi kisan-gilla, dole ne a bar doka ta yi aikinta.
“Kundin Tsarin Mulki ya bai wa kowane wanda ake zargi da laifi haƙƙin samun shari’a ta gaskiya da kuma damar amfani da dukkanin hanyoyin shari’a da doka ta tanada,” in ji shi.
Ya yi gargaɗin cewa kiran da jama’a ke yi na iya haifar da ɗaukar doka a hannu, yana mai jaddada cewa dole ne shari’a ta bi matakan da doka ta tanada, duk da tsananin laifin da aka aikata.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link