Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci don inganta tsaro a Jihar
[ad_1]
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa, Professional Hunters Association of Nigeria (PROHAN), motoci ƙirar Toyota Hilux guda biyu domin ƙara taimaka musu wajen yaƙi da rashin tsaro a jihar.
Gwamnan, ya ce motocin za su taimaka wa ayyukan ƙungiyar wajen yaƙi da satar shanu, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ’yan ta’adda a sassan Jihar.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka wajen saurin kai ɗauki a wuraren da ke fama da matsalar tsaro, tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma.
Da yake magana a madadin ƙungiyar, Shugaban PROHAN na Jihar Gombe, Rabi’u Baushe (Baushen Gombe), ya gode wa Gwamnan bisa tallafin da ya ba su.
Ya ce motocin za su taimaka musu wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
“InshaAllahu, wannan tallafi zai ƙara mana ƙwarin gwiwa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Za mu ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da ’yan ta’adda a faɗin jihar,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar da cewa PROHAN za ta ci gaba da aiki tare da gwamnati da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Gombe.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link