Darajar Tamburan Kasar Sin Sun Karu A Duniya
[ad_1]
Cibiyar kimanta darajar tambura a duniya ta Brand Finance mai mazauni a birnin London, ta yaba sosai da karuwar darajar tamburan kasar Sin a duniya da kuma yadda kasar ke jan hankalin kasa da kasa cikin lumana.
Brand Finance ta bayyana haka ne cikin wasu sabbin rahotanni biyu da ta fitar jiya Talata, a Davos na kasar Switzerland.
Rahoto mai taken Global 500 2026, wanda jeri ne na tambura mafiya karfi da daraja 500 a duniya, ya nuna cewa yawan tamburan kasar Sin da suka shiga jerin ya kai wani sabon mataki. Jimilar tamburan kasar Sin 68 ne suka shiga jerin tambura 500 na duniya, inda suka dauki kaso 15.1 na jimilar jerin.
Ta fuskar yawan tambura dake cikin jerin, kasar Sin ce kasa ta biyu a duniya, inda ta bi bayan Amurka. Galibin tamburan kasar Sin su ne ke jan ragamar bangarorinsu a duniya, musamman a bangarorin fasaha da kayayyakin aiki da harkokin kudi.
Tambarin TikTok ko Douyin na Sin dake gaba-gaba a duniya, ya tsallake mataki 1 zuwa na 6, bayan samun karuwar kaso 45 na darajarsa zuwa dala biliyan 153.5, wanda ya samu daga fadada manhajar da kuma karuwar masu amfani da ita.
Wani rahoto na daban mai taken the Global Soft Power Index 2026, ya nuna cewa Sin ce kasa daya cikin manyan kasashe 10 da makin manufarta ta jan hankalin kasa da kasa cikin lumana ya karu a bana. A cewar Brand Finance, Sin ta samu nasarar ce daga shirye-shiryenta masu dogon zango da suka hada da jarin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da ci gabanta a fannonin kimiyya da fasaha da aiwatar da gyare-gyare masu dorewa da gina tambura a duniya da kuma inganta cudanyar al’adu tsakaninta da kasa da kasa. (FMM)
[ad_2]
Source link