Matasa sun yi zanga-zanga kan yunwa a Adamawa
Wasu gungun matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana a garin Yola da ke Jihar Adamawa, don jan hankalin gwamnati kan ƙaruwar talauci da yunwa.
Masu zanga-zangar sun bin manyan tituna, inda suka yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jihar da su ɗauki matakan rage wahala, rashin aikin yi da matsalar tsaro da ta addabi ƙasa.
Shugaban Ƙungiyar MOTION na Jihar Adamawa, Mista Musa Andrew, ya ce zanga-zangar ta zama dole ne saboda halin matsin tattalin arziƙi da ke ƙara taɓarɓarewa.
“Mun fito ne don mu yi magana kan rashin adalci da wahala, ga yunwa na ƙaruwa,” in ji shi.
“Yawancin ’yan Najeriya suna kwanciya ba tare da cin abinci ba, yara kuma suna zuwa makaranta ba tare da sun ci abinci ba. Rayuwa ta yi tsada sosai.”
Ya kuma bayyana damuwa kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara musamman a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
“Mun gaji da rashin tsaro a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar nan. Yawancin matasanmu, sojoji da ’yan sanda suna rasa rayukansu a kullum,” in ji shi.
Andrew, ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakai don tabbatar da daidaiton rabon albarkatun ƙasa tare da gyara tsarin fansho wanda ya ce yana cike da cin hanci.
“’Yan sanda suna yin ritaya suna komawa gida da kashi 40 cikin 100 na fanshonsu, sauran kuma ana wawurewa. Ba za mu lamunci wannan zalunci ba,” a cewarsa.
Ya kuma nemi a bai wa matasa dama su shiga harkae shugabanci.
“Yawancin shugabanninmu sun fara shugabanci tun suna da shekaru 20, amma yanzu sun ƙi bai wa matasa dama. Shugabanci ba gado ba ne,” in ji shi.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, Hajiya Blessing Musa, ta koka kan tsadar rayuwa, inda ta ce a yanzu magidanta da dama ba sa iya sayan kayan abinci.
“Yunwa tana kashe mu. Farashin kayan abinci ya yi tsada sosai, kuma ba mu da kuɗin saye,” in ji ta.
“Wani mutum ya roƙe ni na sayi shinkafa kan Naira 1,400 amma ba zan iya saya ba. Sama da kashi 70 cikin 100 na ’yan Najeriya suna rayuwa cikin talauci.
“Ba za mu iya tura ’ya’yanmu makarantu masu kyau ba, saboda na gwamnati ba sa aiki yadda ya kamata.”
Ta roƙi gwamnati ta ɗauki matakai don rage talauci, sauƙaƙa farashin abinci da kuma inganta makarantun gwamnati.
Mista Dennis Babangida, wani jagoran matasa, ya bayyana cewa yunwa ta yi ƙamari a Arewa kuma abun damuwa ce.
Ya nemi gwamnati ta tallafa wa manoma da kuma ƙirƙiro ayyukan yi domin rage talauci.
“Farashin taki ya yi tsada sosai, manoma ba sa iya saya. Idan gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma da kuma samar da ayyukan yi, hakan zai rage talauci da yunwa,” in ji Babangida.
Ya kuma gargaɗi gwamnati cewa idan ta ci gaba da yin shiru, matsalar yunwa na iya haddasa rikice-rikice a tsakanin jama’a.
“Jama’a suna jin yunwa kuma suna jin haushi. Gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki kafin lamarin ya fi haka muni,” in ji shi.