Budurwa ta mutu a ɗakin saurayin da ke shirin auren ta a Abuja

[ad_1]



Wta budurwa mai shekaru 24 mai suna Kelechi Ebubechukwu, ta rasu a cikin wani yanayi da mai daure kai a gidan saurayinta da ke Gwagwalada, Babban Birnin Tarayya Abuja.

Wani ƙwararren masani kan tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Talata.

Majiyoyin ’yan sanda sun ce binciken farko ya nuna cewa marigayiyar na fama da zazzabin cizon sauro kafin rasuwarta.

A cewar mjiyoyin, an samu takardar da ke dauke da rubutun magungunan da ake zaton na mai fama da cutar ne a dakin da lamarin ya faru.

Zagazola ya ce, “A ranar 9 ga watan Satumba, an samu rahoton wani lamari mai tayar da hankali na kisan kai a Gwagwalada, bayan wata mata mai shekaru 24 da aka gano sunanta Ebubechukwu Sunday Kelechi ta mutu ba zato ba tsammani a gidan saurayin da za ta aura.”

“Majiyoyi sun ce binciken farko na ’yan sanda ya nuna cewa tana fama da zazzabin cizon sauro kafin rasuwarta, kuma an samu magungunan cutar a wurin. Ba a ga wata alamar tashin hankali a jikinta ba.”

Makama ya kara da cewa an kama saurayin marigayiyar domin fadada bincike don gano ainihin musabbabin rasuwarta.

Lamarin Ebubechukwu dai ya kara yawan jerin matan da suka rasu a gidajen mazajensu ko samarinsu a cikin watannin baya-bayan nan a fadin Najeriya.

Rahotannin ’yan sanda sun nuna cewa yawancin irin wadannan abubuwan na faruwa ne yayin jima’i, yayin da wasu kuma ke da alaka da fada a tsakanin su ko kuma sanadiyyar tashin cututtukan da suke damun su.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *