Gwamnonin Jihohin Kudu Maso Yammacin Nijeriya Sun Jaddada Bukatar Kafa ‘Yansandan Jihohi

[ad_1]


Kungiyar Gwamnonin Kudu-maso-yamma, ta yi kira da a kafa ‘yansandan jihohi, biyo bayan karuwar rashin tsaro a fadin kasar nan.

Gwamnonin sun kuma ja hankalin gwamnatin tarayya, kan abin da ta kira bukatar inganta yanayin dazuzzuka a fadin jihohin yankunan.

Taron ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar ta yi wani abu a kan dimbin dazuzzukan da ta ce, sun zama maboyar ‘yan ta’adda.

A cikin sanarwar, bayan wani taro da suka yi a birnin Ibadan na jihar Oyo, dukkanin gwamnonin shida; sun amince da cewa, gwamnatin tarayya ta taimaka; musamman wajen tura jami’an tsaro na gandun daji zuwa fadin jihohin Kudu-maso-yamma, inda kowace gwamnatin jihar ke da alhakin samar da ma’aikatan da ake bukata.

Shugaban kungiyar, kuma Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ne ya karanta jawabin taron.

Kazalika, wadanda suka halarci taron; sun hada da Gwamnoni Dapo Abiodun na Ogun; Biodun Oyebanji na Ekiti; Lucky Aiyedatiwa na Ondo; Ademola Adeleke na Osun, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Prince Kola Adewusi; da gwamnan mai masaukin baki, Seyi Makinde.

A cikin sanarwar, taron ya amince da kafa asusun tsaro na Kudu-maso-yamma (SWSF), a karkashin Hukumar DAWN, wanda kungiyar masu ba da shawara ta musamman kan harkokin tsaro, na dukkanin jihohin Kudu-maso-yamma, za ta gudanar tare da yin taro a kowane wata.

Domin inganta tattara bayanan sirri da kuma saurin mayar da martani a cikin jihohi shida, dandalin ya dauki hanyar sadarwar ta zamani (dijital) guda daya.

“Zauren ya kudiri aniyar kafa tsarin raba bayanan sirri kai tsaye a tsakanin dukkanin jihohin Kudu-maso-yamma guda shida (Legas, Ogun, Oyo, Osun, Ondo da Ekiti), wannan dandali zai yi musayar sanarwar barazana, taswirar abubuwan da suka faru, sanarwar matafiya da kaya tare da daidaita matakin gaggawa daga jiha zuwa jiha.”

Sanarwar ta kuma nuna damuwa a kan kutsawa dazuzzukan da gungun masu aikata laifuka ke yi, inda ta bukaci taimakon gwamnatin tarayya, wajen tura jami’an gandun dazuzzukan tare da jaddada aniyar gwamnonin na tabbatar da kare dazuzzukan.

Da yake magana a kan matsalar kaura zuwa yankin Kudu-maso-yamma ba tare da ka’ida ba, taron ya jaddada bukatar tsaurara matakan kula da iyakoki da inganta tsarin tantancewa.

“Kungiyar ta kuma nuna matukar damuwa game da yin kaurar, ba bisa ka’ida ba da ke ci gaba da haifar da kalubale a fadin yankin na Kudu-maso- yamma.

Ta kara da cewa, “Zauren ya amince da kara karfafa hadin gwiwar tsaro, domin tabbatar da cewa; tafiye-tafiye tsakanin jihohi, ba zai zama wata hanya ta rashin tsaro ba.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *