Ministan Harkokin Wajen Sin: Babakere Ba Ya Samar Da Mafita

[ad_1]

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron ministoci na farko na tsarin tattaunawa na dabarun “3+3” na harkokin waje, da na tsaron kasa, da na tsaron jama’a tsakanin Sin da Vietnam, wanda ya gudana jiya a birnin Hanoi na kasar Vietnam, tare da jagorantar taron kwamitin jagorancin hadin gwiwa na bangarorin biyu karo na 17, sannan ya zanta da kafafen yada labarai na Sin.

Wang Yi ya gabatar wa manema labarai halin da ake ciki game da tsarin tattaunawa na dabarun “3+3” na Sin da Vietnam, inda ya nuna cewa, bayan taron majalisar NPC da CPPCC na Sin, da kuma taron jam’iyyar kwaminis ta Vietnam karo na 14, nan take bangarorin biyu sun gudanar da taron ministoci na farko na tsarin “3+3”, wanda ya bayyana ingantacciyar dangantakar jam’iyyu da kasashen biyu bisa masu hangen nesa, kuma ya fitar da wata alama cewa, Sin da Vietnam na hada kai don kare tsaron tsarin siyasa, da kuma neman ci gaban kasa tare.

Wang Yi ya ce, a halin yanzu, tsarin kasa da kasa yana canzawa sosai, kuma rikice-rikicen yanki suna yaduwa. Wasu manyan kasashe suna yawan yin amfani da karfi yadda suke so, wanda ke kawo babbar matsala ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Ya ce, fin nuna karfin tuwo a bangaren siyasa ba ta da mafita, kuma babakre ba ya samun goyon bayan jama’a. Sin a matsayinta na muhimmiyar karfin tabbatar da zaman lafiya, da karfin kawo kwanciyar hankali, da kuma karfin nuna adalci a duniya, tana son yin hadin gwiwa da Vietnam da sauran kasashe don gaggauta gina al’ummar Asiya-Pacific ta bai daya, da kuma ba da misali kan gina kyakkyawar makomar bil-Adam ta bai daya. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *