Gobara Ta Hallaka Mutum 2, Ta Lalata Dukiya Ta Biliyan 1.59 A Bauchi

[ad_1]

Ibtila’in gobara ta hallaka mutane biyu tare da lalata kadarorin da darajarta ta kai naira biliyan 1.59 a Jihar Bauchi tsakanin Janairu zuwa Disamba 2025, kamar yadda hukumar kashe gobara ta tarayya (FFS) ta bayyana.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar FFS ta jihar Bauchi, Umar Lawal, ne ya bayyana hakan a cikin rahoton kididdigar gobara da aka fitar ga ‘yan jarida a ranar Litinin a Bauchi.

  • Cinikayyar Waje Ta Jihar Xinjiang Ta Bunkasa A Shekarar 2025
  • Kudaden Bincike Da Samar Da Ci Gaba Na Kamfanonin Gwamnatin Sin Sun Ci Gaba Da Haura Yuan Tiriliyan Daya Cikin Shekaru Hudu A Jere

A cewarsa, hukumar ta amsa kiran gaggawa domin ta zo ta kashe gobara guda 167 a tsakanin wannan lokacin, inda aka ceto rayukan mutane hudu tare da kare kadarorin da darajarta ta kai Naira biliyan 2.86 daga lalacewa.

Ya bayyana cewa gobarar ta shafi gine-ginen jama’a da na gwamnati, gidajen masu zaman kansu, cibiyoyin ilimi, kasuwanni, tashoshin man fetur da iskar gas, da kuma motoci a fadin jihar.

Yayin da ya ke yin bayani dalla-dalla, Lawal ya ce gobara guda 10 sun auku a gine-ginen jama’a da na gwamnati, inda aka yi asarar dukiya mai darajar Naira miliyan 23, yayin da aka ceto kadarori da darajarsu ta kai Naira miliyan 855.1.

Ya kara da cewa an samu gobara guda 80 a gidajen masu zaman kansu, lamarin da ya janyo lalacewar dukiya na Naira miliyan 605, yayin da aka ceto dukiya ta kai Naira biliyan 1.4.

Ya kuma ce gobara a cibiyoyin ilimi ta lalata kadarorin Naira miliyan 120, yayin da aka ceto Naira miliyan 200, “An samu gobara guda biyar a kasuwanni, inda aka yi asarar kadarorin Naira miliyan 45, yayin da aka ceto Naira miliyan 90,” in ji shi.

Lawal ya kara da cewa gobara guda 15 sun shafi tashoshin man fetur da iskar gas, inda aka yi asarar Naira miliyan 23.7, yayin da aka ceto kadarorin Naira miliyan 53.

Ya ce kuma an samu wasu gobara guda 15 da suka shafi motoci, inda aka lalata dukiya mai darajar Naira miliyan 70, yayin da aka ceto Naira miliyan 33.

Mai magana da yawun FFS ya danganta yawancin gobarar da matsalar kayan lantarki, tashin wutar lantarki (power surge), adana man fetur ba bisa ka’ida ba da hatsarori.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *