’Yan sanda sun harbe ’yan bindiga 4 a Binuwai
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai, sun kashe wasu ’yan bindiga huɗu bayan sun kai hari wani shingen binciken ’yan sanda a garin Orokam da ke Ƙaramar Hukumar Ogbadigbo.
Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ta ce lamarin ya faru ne ranar Laraba lokacin da jami’an Operation Zenda Joint Task Force ke aiki a shingen.
Ta bayyana cewa jami’an sun tsayar da wata mota ƙirar Golf 3 baƙa a misalin ƙarfe 5 na yamma domin gudanar bincike, amma mutanen da ke cikin motar sun ƙi yarda a duba motar.
A cewarta, biyu daga cikin mutanen sun fito da bindigogi ƙirar AK-47 suka fara harbin jami’an ’yan sandan yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
’Yan sandan sun yi musayar wuta da su, inda suka kashe ’yan bindiga huɗu, yayin da ɗaya ya tsere cikin daji.
An ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, harsashi 15, motar ƙirar Golf 3 baƙa, da wasu kayayyaki da ake zargin na tsafi ne.
DSP Edet, ta ce rundunar ta fara bincike tare da ƙoƙarin kamo wanda ya tsere.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ifeanyi Emenari, ya yaba wa jami’an bisa jarumta da ƙwarewa a aikinsu.
Ya tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da aikata laifuka tare da kare rayuka da dukiyoyinsu.
Ya kuma buƙaci jama’a da su kasance masu bin doka da oda, tare da bai wa ’yan sanda sahihan bayanai domin ƙara inganta tsaro a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link