Tinubu Ya Yaba da Jagorancin Gwamna Abba Yusuf Yayin Da Ya Cika Shekara 63
[ad_1]
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, murnar cika shekara 63 a duniya, a ranar Litinin, 5 ga Janairu, 2026. Tinubu ya aike da sakon taya murnar ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi.
A cikin sanarwar, Shugaban ƙasar ya yabawa Gwamna Yusuf bisa gaskiya, da sauƙin kai, da ƙasƙantar da kai da kuma jajircewarsa wajen hidimar jama’a, kamar yadda ya bayyana a salon mulkinsa a Jihar Kano. Tinubu ya ce waɗannan halaye sun bayyana ƙarara a yadda gwamnan ke tafiyar da harkokin jihar tun bayan hawansa mulki.
- Lee Jae-Myung: Tabbas Za A Kyautata Hulda Tsakanin Koriya Ta Kudu Da Sin
- Tinubu Ya Sha Alwashin Adalci Ga Waɗanda Aka Kashe A Kasuwar Neja
Gwamna Yusuf, wanda aka zaɓe shi a shekarar 2023 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya taba riƙe muƙamin Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri a Jihar Kano daga 2011 zuwa 2015 a zamanin tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso. Shugaba Tinubu ya bayyana cewa mulkin Yusuf na ci gaba da raya aƙidar siyasar ci gaba da mayar da hankali kan talakawa, kamar yadda marigayi Malam Aminu Kano ya assasa a jihar.
Shugaban ƙasar ya ce kwarewar shugabanci da Gwamna Yusuf ya samu a baya ta taimaka masa wajen aiwatar da sauye-sauyen more rayuwa da ake gani a Kano, ciki har da shirye-shiryen sabunta birane, gina gadoji da hanyoyi, har da gina hanyoyi masu tsawon kilomita biyar a kowace karamar hukuma. Ya kuma yaba da ayyana dokar ta-ɓaci a bangaren ilimi, wanda ya haifar da ƙarin nasarar ɗaliban Kano a jarabawar NECO, tare da yi wa gwamnan fatan tsawon rai da karin nasarori a shugabancinsa.
[ad_2]
Source link