Mutfwang ya aike wa majalisar dokokin Filato ƙarin kasafin kuɗin N74bn
[ad_1]
Majalisar Dokokin Jihar Filato ta karɓi ƙarin kasafin kuɗin Naira biliyan 74.6 domin shekarar 2025.
Gwamna Caleb Mutfwang ne, ya aike da buƙatar ƙarin cikin wasiƙa, wacce Kakakin Majalisa, Rt. Hon. Naanlong Daniel, ya karanta a zaman majalisar na ranar Juma’a.
A cikin wasiƙar, gwamnan ya bayyana cewa kuɗin zai fito daga harajin da jihar za ta tara, kuma za a fi mayar da hankali wajen gina manyan abubuwan more rayuwa da kuma ƙarfafa haɗin kan jama’a a jihar.
Bayan karanta wasiƙar, Jagoran Majalisa, Hon. Joseph Gokum, ya nemi a aiwatar da ƙudirin kasafin.
Mambobin majalisar sun amince ta hanyar kaɗa ƙuri’ar murya.
Ƙudirin ya wuce karatu na farko da na biyu, sannan Kakakin ya tura shi zuwa Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar, inda ya umarce su da su yi aiki tare da sauran kwamitoci domin nazarin ƙudirin, sannan su kawo shawarwari.
Majalisar ta kuma tattauna kan guguwar da ta shafi yankin Foron a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi.
Mambobin sun amince a aike da ƙudurinsu ga hukumomin da abin ya shafa.
Kakakin Majalisar, Daniel, ya yaba wa mambobin bisa jajircewarsu, sannan ya buƙaci da su ci gaba da aiki don ci gaba da walwalar Jihar Filato.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link