An kwantar da jarumin fina-finan Amurka Chuck Norris a asibiti
[ad_1]
Rahotanni na cewa an kwantar da fitaccen jarumin fina-finan faɗa a masana’antar Hollywood ta Amurka, Chuck Norris, a wani asibiti a Jihar Hawaii sakamakon rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
Bayanai sun ce, an garzaya da jarumin zuwa asibiti ne a tsibirin Kauai cikin gaggawa, sai dai an ce yana cikin yanayi mai kyau duk da rashin lafiyar da yake fuskanta.
Har yanzu wakilan Norris ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.
Jarumin, wanda ya cika shekaru 86 a makon da ya gabata, ya yi murnar zagayowar ranar haihuwarsa da wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta, inda ya nuna yana dambe, yana mai cewa: “Ba na tsufa, sai dai na ƙara ƙarfi.”
Chuck Norris ya shahara ne bayan soma fitowarsa a fina-finai tun shekarar 1968, sannan ya ƙara yin fice bayan fafatawarsa da fitaccen gwarzon kung-fu, Bruce Lee, a fim ɗin The Way of the Dragon.
Ana kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun jaruman fina-finan faɗa da suka yi tasiri a duniya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link