Ministan Tsaron Nijeriya Ya Taya Al’ummar Musulmai Murnar Sallah

[ad_1]

Mai Girma Ministan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya taya al’ummar Musulmai murnar kammala azumin watan Ramadan lafiya da bikin karamar Sallah.

Ministan ya taya al’ummar Musulai murnar ne tare da jan hankalinsu su dukufa wajen addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar da sanya shugabanni cikin addu’o’insu, domin samun mafita da nasarori kan tarin kalubalan da kasar ke fuskanta.

  • Ana Neman Hankada Yankin Gabas Ta Tsakiya Cikin Mummunan Rami In Ji Wakilin Kasar Sin
  • Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Sauya Fasalin Tsarin Tsaro A Yaki Da Ta’addanci

Sannan ya bukaci su yi addu’oi na musamman kan zaben 2027, wajen samun lafiya a lokaci yi da kuma kammalawa.

Haka kuma ministan ya jan hankalin al’ummar Musulmai da su yi amfani da darrusan da suka koya a watan Ramadan, kamar hakuri, juriya, kokarin ibadah, taimako, kyauta da sadaka, tausayin juna, jin kai, sadaukarwa da mika wuya ga umarnin Allah a rayuwarsu ta yau da kullum, domin samun nasarori a rayuwa da gamawa da duniya lafiya.

Kamar yadda ya sha kira da jan hankalin al’ummah kan sha’anin tsaron dukiyoyi da rayukan ‘yan kasa wanda ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, ministan ya bukaci daukacin al’ummar Nijeriya da su yi mai yiwuwa da zage dantse wajen bayar da gudunmawa domin tabbatar da ingantaccen tsaro a kasar.

A yayin da a nasa bangaren ya maida hankali da jajircewa wajen lalubo bakin zaren da dinke matsalolin tsaron kasar, ya bukaci al’ummar Musulmai da su ci gaba da sanya shi cikin addu’o’insu na yau da kullum, domin ya sami nasara a ayyukan da ya sa a gabansa na tsaron kasar

Haka zalika, ministan ya yi wa Musulman Nijeriya da Kiristoci godiya kan irin soyayya da kauna da goyon baya da kulawa da addu’o’in da suke yi masa a kullum. Ya ce da yardar Allah zai ci gaba da aiki ba dare ba rana domin samar da tsaron da ake bukata a kasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *