Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa

[ad_1]



Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara da wasu Dattawan Jihar Ribas.

Mai taimaka wa Wike kan yaɗa labarai, Lere Olayinka ne, ya wallafa hoton ganawar a shafukan sada zumunta, inda ya ce kakakin Majalisar Dokokin jihar, Martin Amaewhule, ya halarci taron.

Ko da yake Olayinka bai bayyana abin da aka tattauna a taron ba, amma wannan ce ganawa ta farko da aka yi tsakanin Wike da Fubara tun bayan da gwamnan ya kori wasu daga cikin muƙarrabansa yayin da yake shirin kafa sabuwar majalisar zartarwa a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa naɗa sabbin kwamishinoni na daga cikin yarjejeniyar sulhu da Shugaba Bola Tinubu ya yi tsakanin Wike da Fubara lokacin da ake tsaka da rikicin siyasa a jihar.

A yayin wani taron ban kwana da tsofaffin Kwamishinoni a Fadar Gwamnatin jihar da kw Fatakwal a ranar Laraba, Gwamna Fubara ya ce an tilasta masa sallamar muƙarrabansa saboda hukuncin Kotun Ƙoli da ya shafi naɗinsu.

A farkon shekarar nan ne, Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa Majalisar Dokokin da ke goyon bayan Wike ce halastacciya ce.

A lokacin da rikicin siyasar ya yi ƙamari a jihar, wasu daga cikin muƙarraban Fubara sun samu tantancewa daga ɓangaren majalisar da Victor Oko-Jumbo ke jagoranta, amma tsahin Wike bai amince da hakan ba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Nelson Chukwudi, ya fitar, ya ce Fubara ya gode wa tsofaffin kwamishinonin bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.

Gwamnan, ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai da Shugaba Tinubu wajen gina ƙasa mai cike da zaman lafiya da ci gaba.

Ya ƙara da cewa zai ci gaba da yi wa Jihar Ribas hidima, tare da yi wa ’yan kasa fatan alheri a bikin ranar samum ’yancin kai.

Sanarwar ta ƙara da cewa, dukkanin kwamishinoni da jami’an gwamnati da hukuncin Kotun Ƙoli ya shafa, an sallame su daga muƙamansu nan take.

Bayan ƙarewar dokar ta-ɓaci, ’yan majalisar jihar, sun buƙaci Gwamna Fubara da ya miƙa sunayen sabbin kwamishinoni.

Ana sa ran gwamnan zai kafa sabuwar majalisar zartarwa nan ba da jimawa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *