2027: Gwamna Lawal Ya Umurci Masu Neman Takara Su Yi Murabus
[ad_1]
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya umarci masu riƙe da muƙaman gwamnati su yi murabus. Umarnin ya shafi waɗanda ke shirin tsayawa takara a 2027.
An fitar da umarnin ne a taron Majalisar Zartarwa karo na 64 a Gusau. Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya tabbatar da hakan.
- Rikice-rikicen Da Suka Addabi PDP Ne Suka Sa Na Koma APC — Gwamnan Zamfara
- An Cire Tutar PDP A Fadar Gwamnatin Zamfara, A Shirin Sauya Sheƙa Zuwa APC
Sanarwar ta ce matakin ya dace da dokar zaɓe da jadawalin INEC. Ta jaddada cewa dole ne masu burin takara su bar muƙamansu kafin lokaci.
Gwamnan ya buƙaci dukkan mambobin majalisar da su sauka kafin 31 ga Maris, 2026. Ya ce hakan zai ba da dama ga bin ƙa’idojin zaɓe yadda ya kamata.
Haka kuma ya umarci Sakataren Gwamnati ya fitar da sanarwa ga masu muƙaman siyasa. Wannan na nufin tabbatar da kowa ya bi umarnin da aka bayar.
[ad_2]
Source link