Ɗan shekara 3 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano

[ad_1]



Wani yaro ɗan shekara uku a duniya mai suna Abdura’uf Badamasi, ya rasu bayan da ya faɗa cikin wata rijiya a ƙauyen Wangara da ke Ƙaramar Hukumar Tofa a Jihar Kano.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 7:50 na safiyar ranar Juma’a, 30 ga watan Janairu.

Wani mai suna Dan Asabe Rabiu ne ya kira ya sanar da faruwar lamarin.

Nan take hukumar ta tura jami’anta zuwa ƙauyen.

Bayan isar su, mazauna ƙauyen sun shaida musu cewa an daɗe ana neman yaron tun yammacin ranar Alhamis.

Iyayensa na zargin cewa mai yiwuwa ya faɗa cikin wata rijiya da ke ƙauyen ne.

Jami’an kashe gobara sun shiga cikin rijiyar tare da fito da yaron, amma sun same shi a sume.

Daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.

An miƙa gawar yaron ga mai garin ƙauyen Wangara kamar yadda doka ta tanada.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan yaron tare da jan hankalin jama’a da su riƙa kula da motsin yara daga wurare masu hatsari.

Hukumar ta kuma buƙaci al’umma da suke rufe rijiyoyinsu yadda ya kamata domin kaucewa sake faruwar irin wannan iftila’i a gaba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *