Kirsimeti: Gidauniya ta bai wa Kiristoci kyautar buhun shinkafa 600 a Gombe

[ad_1]



Gidauniyar Velocity Humanitarian Foundation ta raba buhun shinkafa 600 ga Kiristoci a Jihar Gombe, domin murnar bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Ta raba buhun shinkafa mai nauyin kilo 25, kuma an miƙa tallafin ne ga Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen Jihar Gombe.

Da yake miƙa tallafin, Shugaban Kwamitin Gidauniyar, Adamu Aliyu Ibrahim, ya ce sun yi hakan ne a madadin wanda ya kafa gidauniyar, Injiniya Aliyu Muhammad Kombat, domin nuna ƙauna, haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai.

Ya ce gidauniyar ta ga dacewar raba abin da Allah Ya ba ta domin faranta ran Kiristoci.

Ya ƙara da cewa ko da yake gidauniyar sabuwa ce, amma ta ƙudiri aniyar tallafa wa mabuƙata a jihar.

A nasa jawabin, Shugaban CAN na Jihar Gombe, Rabaran Father Joseph Alphonse Shinga, ya gode wa gidauniyar bisa wannan tallafi.

Ya ce tallafin ya zo a lokacin da ya dace, musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Rabaran Shinga ya yi kira ga Kiristocin da suka amfana da tallafin da su yi addu’a domin zaman lafiya a Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.

Ya kuma bukaci sauran masu hannu da shuni da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su riƙa taimaka wa marasa galihu, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa.

A cewarsa, Kirsimeti lokaci ne na farin ciki, addu’a da taimakon juna.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *