Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Kasar Sin Sun Samun Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba a Watanni 11 Na Farkon Bana

[ad_1]

Taron shugabannin kamfanoni mallakar gwamnatin kasar Sin da aka gudanar a kwanan nan ya ba da labari cewa, a shekarar 2025, kamfanonin sun aiwatar da ayyukan inganta da kyautata karfin tattalin arziki da dai sauran makamancin ayyuka, inda suka samu bunkasa yadda ya kamata ba tare da tangarda ba. A cikin watanni 11 na farkon bana, karuwar kudin da kamfanoni suka samu ta kai Yuan tiriliyan 9.5, wadda ta karu da kashi 1.4% idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.

Daga watan Janairu zuwa Nuwamba, yawan jarin da kamfanonin suka zuba ga kadarori (ban da kadarorin gidaje) ya kai Yuan tiriliyan 3.3, wanda ya karu da kashi 0.7%. Dukkansu sun kara karfafa bincike da kirkire-kirkire da kansu, inda yawan kudin da aka kashe na bincike ya kai kashi 2.62%.

Bayanan sun nuna cewa, a lokacin shirin raya ci gaban kasar Sin da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 14, jimillar kadarorin kamfanoni mallakar gwamnatin kasar Sin ta ci gaba karuwa, inda ta haura adadin kudi Yuan tiriliyan 70, 80, da 90 bi-da-bi, kuma yanayin girmansu, da ikon samar da kayayyaki da hidimomi da tasirin tamburansu sun kara karfi sosai.(Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *