Batun Sauya Sheka Da Makomar Dimokiradiyyar Nijeriya  A 2027

[ad_1]

A yayin da Nijeriya ke shirye-shiyen shiga wani sabon zango na tunkarar zabukan shekarar 2027, ‘yan siyasa, masu rike da madafun iko, sai  kai Gwauro da Mari suke ta faman yi, domin ci gaba da rike ikonsu, inda wasun su kuma suke ta sauya sheka zuwa wasu jamiyyu, domin dai, su ga sun tsallake siradin, na 2027.

Koda yake, wannan halin, ba sabon abu ne, fannin siyasar kasar ba, amma abinda yake sabo ga batun shi ne, ganin yadda kota halin kaka, masu rike da madafun ikon, suke son ci gaba da rike madafun na su, na ikon.

  • Majalisar Dattawa Ta Kai Ta’aziyya Ga Al’ummar Kurmin Wali, Ta Yi Alkawarin Kayan Agaji
  • Hotuna: Babbar Mota Ta Hallaka Wata Bafulatana A Bauchi

Akasarin wadannan ‘yan siyasar da ke a cikin jami’yyun adawa, na dai ganin sauya sheka zuwa jami’iyya mai mulki, shi ne, kawai mafita, a gare su, matukar suna son ci gaba da jan ragamar alumominsu, da suka jagoranta.

Misali, akalla Gwamnonin hudu na jam’iyyar PDP, a  watan Disambar 2025, suka sauya sheka, inda suka danganta cewa, sun yi hakan ne, saboda rikice-rikiecen cikin gida, a PDP, inda daga baya, wasu Gwamnoni biyu, suma, suka bi sahu.

Kazalika, sauya sheka da Gwamnan jihar Knao da aka zaba a inuwar jam’iyyar NNPP zuwa jami’iyyar APC, hakan ya kawo karshen rade-radin da ake yi, cewa, Abba Kabir Yusuf, zai sauya sheka.

Za a dai iya cewa, a jamhuriya ta hudu, akasarin tsare-tsare da sauran shiye-shiye irin na shugabanci a tsakanin jam’iyyu, kusan duk sun kau.

Hakan ya sanya, jami’iyyun tamkar su zamo  wani Tsani na kawai neman takara da tattaunawa tare da hada-hadar Tikitin neman tsayawa takara.

A gafe daya kuma, an shafe shekaru, kotuna na shiga tsakanin jami’iyyu, idan an samu wata takaddama, a yayin da aka gudanar da zabukan fidda gwani.

A saboda kaucewa duk wani tirniki, da ‘yan siyasa, musamman ‘yan takara suke ganin za su fuskanta, hakan ya sanya, suke kokarin sauya sheka, domin samun kai wa, ga tudun mun tsira.

Mulkin Dimokiradiyya dai, ya dogara ne kachokam, kan sasantawa a cikin sauki, a tsakanin ‘yan takara, inda su kuma masu kada kuri’a ke barge gumisnu, ta hanyar zabar wanda suke ra’yi, a ranar zabe.

Hakazalika, a daidai lokacin da zabukan 2027 ke kara karatowa, inda a lokacin ne, ‘yan Nijeriya ya kamata su yanke hukuncin wanda ya fi cancanta ya shugabance su, amma abin takaici, sai dai kawai, ‘yan siyasar, su shige daki su yi kukus kan wanda zai tsaya takara, ba tare da gudanar da yin yakin neman zabe ba.

Wannan ya kara haifar da rashin amincewa, a zuciyar ‘yan kasar da kuma kara durkuasar da Dimokiradiyyar kasar.

Kazalika, a kasar akwai matsin tattalin arziki da rashin gamsuwa, musamman a tsakanin matasa, wanda hakan ke haifar da rauni, ga sakamakon zabe.

Mai makon ‘yan siyasar su rinka janyo masu jefa kuri’a a jiki da nuna gaskiya, amma sun buge da sauya sheka, zuwa wata jami’yya.

Wannan yawan sauya shekar, na janyo babbar illa ga tsari da akidar samar da ci gaba a kasa.

Hakazalika, ba wai lallai sai bangaren shari’a, ya shiga tsakanin duk wata takadda da ta kunno kai a cikin jam’iyyu ba, domin abu ne, su jami’iyyun za su iya lalubo da mafita.

Shigar da bangaren shari’a a duk wata tataburza ta rikicin da ya kunno kai a cikin wata jami’iyya hakan kan shafi kima da kuma martabar bangren na shari’a, inda hakan zai kuma zubar da mutucin bangaren, a idon ‘yan kasa.

Nijeriya dai, ba za iya samar da kinshikin Dimokiradiyya mai dore ba, matukar,  ‘yan siyasar kasar, za su ci gaba da sauya sheka, zuwa wata jami’yya.

Ya zama wajbi, jami’yyun kasar su tabbatar da sun karfafa Dimokiradiyya a cikin jami’yyunsu da kara karfafa kundin tsarin mulkin jami’iyyunsu, tare da daukar mataki, ga duk ‘yan jami’yyar da suka sauya sheka.

Dole a rinka yin gaskiya a yayin zaben fidda gwani kuma dole ‘ya’yan jami’iyyun su san da cewa, suna da hakki a yayin gudanar zaben fidda gwani, jami’iyyunsu.

Bugu da kari, suma sauran hukumomin da ke sanya ido, a kasar, akiwar rawar da za su iya takawa, kan batun.

Wabi ne batun sauye-sayen dokar zabe, ta wuce batu ne na tabbatar da ladarbarwa da cikn ka’ida, a tsakanin jam’iyyu.

Bayar da ‘yanci fadar ra’ayi ga kungiyoyi, abu ne da ke da matukar mahaimmanci, domin idan babu hakan, akwai matsala.

Mulin Dimokiradiyya na ginawa ne kawai, daga bangaren masu kada kuri’a, ba wai a tsakanin ‘yan siyasa, su kadai ba.

Zabukan na 2027, za su kasance tamkar gwajin dafi ne, ga jami’iyyun kasar, inda hukuncin da jami’yyun da ‘yan siyasa da kutuna da kuma masu kada kuri’a, za su kan wanda wanda zai samu nasara.

Irin wannan salon na sauya sheka, matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, hakan ko dai ya haifar da alfanu na gajeren zango ko ma, na dogon zango.

Nijiya dai, na cikin tsaka mai wuya, dangane da zabukan na 2027, da ke kara karatowa.

Alamu dai na nuna cewa, irin wannan sauya shekar da ‘yan siyasar ke ci gaba da yi, akwai yuwuar, za a jingine batun ‘yancin masu jefa kuri’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *