An yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu da Iran a Birtaniya
[ad_1]
Ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a birnin Landan na Birtaniya, duk da cewa gwamnati ta haramta gudanar da gangamin jama’a saboda dalilan tsaro.
’Yan sanda sun ce an kama mutum 12 yayin zanga-zangar, tare da buɗe bincike kan wasu kalaman adawa da Isra’ila da aka yi a wajen gangamin.
Ministar harkokin cikin gida ta Birtaniya, Shabana Mahmood, ta ce an haramta gangamin jama’ar ne domin kauce wa tarzoma, musamman a lokacin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta bayan hare-haren da Iran ke kaiwa a matsayin martani ga farmakin Amurka da Isra’ila.
Hukumar ’yan sanda ta Metropolitan Police ta ce wannan shi ne karon farko da aka haramta irin wannan zanga-zanga a Landan tun shekara ta 2012, sai dai an ba da damar gudanar da taro a wuri guda ba tare da yin gangami ba.
’Yan sanda sun shiga tsakanin masu zanga-zangar kashi biyu masu adawa da juna ta hanyar barin kowanne ɓangare ya yi nasa gangamin a gefuna biyu na Kogin Thames da ke daura da majalisar dokokin ƙasar.
Masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu sun ɗaga tutoci da alluna da ke ɗauke da rubutun kalamai kamar “A dakatar da laifukan yaƙin Isra’ila”, suna mai nuni da farmakin da Isra’ila ke yi a Zirin Gaza tun bayan harin da aka kai ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Wata mata mai shekaru 81, Jean Apps, ta ce ta halarci zanga-zangar ne saboda abin da ta kira rashin adalcin da ake yi wa Falasɗinawa, da kuma hare-haren da ake kai wa Iran.
A gefe guda kuma, masu zanga-zangar adawa da su sun ɗaga tutocin Amurka da Isra’ila tare da tuta mai tambarin “Zaki da Rana” ta Iran, suna jaddada goyon baya ga Reza Pahlavi, ɗan tsohon sarkin ƙarshe na Iran da ke zaman gudun hijira tun bayan juyin juya halin 1979.
Waɗanda suka shirya zanga-zangar ta Ranar Al-Qudus, wato ƙungiyar Islamic Human Rights Commission, sun soki matakin hana zanga-zanga, suna mai cewa matakin na da alaƙa da siyasa.
[ad_2]
Source link