’Yan Boko Haram sun sake kai hari sansanin soji a Borno

[ad_1]



Ana fargabar cewa wasu da ake zargi mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari wani sansanin soja da ke Ajilari, wajen birnin Maiduguri a Jihar Borno.

Rahotanni sun ce harin ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na dare, wanda ya kuma ya faru a lokaci guda da wani hari da ’yan ta’addan suka kai wamo a sansanin soji da ke Baga, inda suka yi artabu da dakarun soji.

Sai dai Aminiya ta ruwaito cewa, wata rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro da ta haɗa da sojoji, ’yan sanda, ’yan sa-kai da kuma rundunar sojin sama ta kai ɗauki cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa jami’an tsaro sun tari hanzari maharan.

Wasu mazauna yankin sun ce sun tsinci kansu cikin tsananin firgici yayin da ƙarar harbe-harbe ta karaɗe ko’ina, da daidai lokacin da jiragen sama masu saukar ungulu ke shawagi a sama.

“Mun ji tsorata sosai. Saboda ƙarar harbe-harbe ta karaɗe ko’ina. Amma AlhamdulilLah yanzu lamarin ya lafa, an kuma ci gaba da sallar dare,” in ji wani mazaunin Gomari, Bashir Yusuf.

A ‘yan kwanakin nan dai ‘yan ta’addan na ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin sojoji a yankin.

A makon da ya gabata ne Ministan Tsaro, Christopher Musa ya gayyaci hafsoshin tsaron Najeriya zuwa wani taron gaggawa, inda daga bisani suka gana da Shugaba Bola Tinubu tare da manyan jami’an tsaro.

Bayan taron, Minstan ya bayyana cewa shugabannin tsaron sun yanke shawarar sauya dabarun yaƙi, yayin da shugaban ƙasar ya ba da umarnin a gaggauta samar da sabbin kayan aiki domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *