’Yan sanda sun kama ɗan bindiga, sun ceto mutanen da aka sace a Kebbi

[ad_1]



Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi, ta kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane tare da ceto mutum biyu a Ƙananan Hukumomin Kalgo da Dandi na jihar.

Kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya ce ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Alhaji Juli Muhammad mai shekaru 55, an sato shi a gidansa da ke ƙauyen Kokani a Kalgo.

An ɗaure shi da sarƙa sannan aka kai shi cikin daji.

Mutum na biyu kuwa, mai suna Garba Bachal mai shekaru 50, an sato shi a ƙauyen Maigwaza da ke Ƙaramar Hukumar Dandi.

SP Usman, ya ce jami’an ’yan sanda daga sashen Kalgo da Kamba, tare da haɗin gwiwar ’yan banga ne suka ceto waɗanda aka sace.

A yayin samamen, sun kama wani da ake zargin ɗan bindiga ne, mai suna Umar Usman daga yankin Augie Fadama na jihar.

Ya ƙara da cewa sauran waɗanda ake zargi sun tsere yayin da suka hangi ’yan sanda, lamarin da ya ba su damar ceto waɗanda aka sace.

An kai Garba Bachal zuwa Asibitin Maigwaza, inda ake kula da lafiyarsa.

SP Usman, ya tabbatar wa al’umma cewa suna ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran waɗanda suka tsere.

Ya ce wannan nasara na nuna ƙudirin rundunar wajen amfani da bayanan sirri da ɗaukar mataki domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *