Pantami Ya Roƙi El-Rufai, Ribadu Da Uba Sani Su Sulhunta A Jana’izar Mahaifiyarsa

[ad_1]

Sheikh Dr. Isa Pantami ya buƙaci Malam Nasir El-Rufai da abokan siyasarsa su ajiye saɓanin da ke tsakaninsu, ya yi wannan kiran ne a makabarta yayin binne mahaifiyar El-Rufai, Hajiya Umma, a Abuja.

Pantami ya yi wannan kira ne a huɗubarsa a maƙabartar Gudu ranar Lahadi. Ya roƙi shugabanni su fifita haɗin kai tare da tunawa da alherin da suka yi wa juna.

  • Dalilin Karuwar Garkuwa Da Mutane Duk Da Hada Layukan Waya Da Lambar NIN – Pantami
  • Dabarun Cafke ‘Yan Ta’adda Cikin Sauki A Nijeriya – Pantami

Ya jaddada cewa rayuwa mai wucewa ce kuma dole kowa ya bar duniya wata rana. Ya ƙara da cewa nasara na zuwa ne ta bin hanyar Allah ba dabarun siyasa ba.

A wurin jana’izar, manyan ‘yan siyasa da dama sun halarta ciki har da Uba Sani da Nuhu Ribadu. Haka kuma an gudanar da sallar jana’iza a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

Rahotanni sun ce mahaifiyar El-Rufai ta rasu a Masar ranar Juma’a. Lamarin ya zo yayin da yake fuskantar shari’a kan zargin kuɗaɗe a kotu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *