Sojojin Ruwa Da Na Sama Na Sin Sun Yi Sintiri A Yankin Huangyan Dao

[ad_1]

Rukunonin sojojin ruwa da na sama na babbar rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin mai kula da shiyyar kudanci, sun gudanar da sintiri na shan damarar yaki a yankin ruwa da sararin samaniya na Huangyan Dao na kasar Sin da sauran yankunan da ke kewaye da shi a yau Lahadi.

Da take jaddada cewa Huangyan Dao wani bangare ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba, rundunar ta shiyya ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, rukunonin sojinta na ruwa da na sama sun kara kaimi wajen sintiri na shan damarar yaki tun daga farkon watan Maris, kuma sun gudanar da ayyuka na bin diddigi, da sa-ido, da gargadi da kuma korar masu shisshigi kamar yadda doka ta tanada.

Rundunar ta kara da cewa, “Wadannan ayyuka na sintiri suna zama wata ingantacciyar hanya ta mayar da martani ga kowane irin take hakki da ayyukan tayar da zaune tsaye.”

Haka kuma duk dai a yau Lahadi, rundunar dakarun kare yankunan ruwa, watau CCG a takaice, ta gudanar da sintirin tabbatar da doka a yankin ruwa na Huangyan Dao na kasar Sin da kuma yankunan da ke kewaye da shi. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *