Sin Ta Bayyana Takaicin Karewar Wa’adin Yarjejeniyar Nukiliyar Amurka Da Rasha

[ad_1]

Kasar Sin ta bayyana takaici bisa karewar wa’adin yarjejeniyar rage yawan makaman nukiliya mai lakabin “New START” tsakanin Amurka da Rasha, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian, ya bayyana a yau Alhamis.

A yayin taron manema labaru na yau da kullum, Lin ya ce yarjejeniyar New START tana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da daidaiton dabarun tsaro na duniya. Ya kara da cewa al’ummar duniya tana nuna damuwa sosai cewa karewar wa’adin wannan yarjejeniya, za ta haifar da illa ga tsarin kula da makaman yaki na duniya da kuma tsarin kula da nukiliya na duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *