Bukatar A Kawo Karshen Cunkoso A Gidajen Gyaran Hali A Nijeriya

[ad_1]

Bisa wasu alkaluma da Hukumar Kiddiiga ta Kasa wato NBS ta fitar, sun tabbatar da cewa, duk wanda ya kai ziyara a gidajen gidan gyaran hali na kasar nan, abinda zai fara tozali da shi, shi ne, irin tsabagen matsalar cunkoson da ake fusaknata, a gidajen.

Wannan ya saba matuka, kan yadda a gina gidajen da kuma yawan adadin masu zaman Jarun, da aka kayyade, za a garkame a cikin gidajen.

  • GDPn Nijeriya Ya Yi Ƙasa Fiye da Na Shekaru 20 da Suka Wuce A Zamanin Obasanjo — Hashim
  • Sinawa Masu Amfani Da Yanar Gizo Sun Kai Biliyan 1.125

A cewar, rahoton NBS kan kididdigr Hukumar Kula da Gidajen Gidan Hali ta kasa, jmilar masu zaman gidajen, ya karu daga 69,946 a 2017, zuwa 81,710, zango na biyu na 2025.

Wadannan alkaluman, sun nuna sun kai, kaso 16.82, inda karuwar ta kai ta sama da shekaru takwas da suka wuce, wanda hakan ya nuna cewa, tsarin, na kula da gidajen, ya kara lalacewa.

Sai dai, a yanzu, yawan wannan adadin a yanzu, ya zarce wanda ake da shi, a yanzu.

Kazalika, kalubalen na cunkson ne, ya haifar da tabarwarewar gidajen, inda gidajen, suka koma tamkar, wani waje, na ajiya mutane da ba a yanke masu hukunci ba.

Misali, gidan gyarn hali na jihar Legas na dauke da masu zaman Jarun guda 9,209 wanda a bisa ka’ida, an tsara za a iya ajiye, masu zaman Jarun guda 4,167 ne kawai.

Wannan ya nuna cunkoson, ya kai kaso of 221 wanda hakan, ya rubanya har sau biyu, na adadin masu zaman gidan da ya kamata a ajiye.

Jihar Ogun kuma na da masu zaman gidan gyran halin da suka kai 4,939, Kano na da 4,667, inda Enugu kuma, ke da 3,536.

Hakan ya nuna cewa, wadannan gidajen, sun tashi da sunan gidajen gyran hali, amma sun koma tamkar, wajen ajiye dabbobi, saboda rashin samun kulawa da masu zama a gidajen da kuma rashin dakunan kwana.

Batun aikin kara gina wasu gidajen daga 53,752 zuwa 65,035 aka yi niyyar yi yin aikin a 2017 zuwa 2025, batun ya kasance, kawai, rubutu ne a kan takarda, da a wamzar da shi ba, inda hakan ya nuna karuwar, ta karu zuwa kaso 20.99.

Ya sama wajibi, hukumomi su jajirce, wajen magance wannan kalubalen, musamman ta hanyar kara gina wasu sabbin gidajen.

Daga cikin wannan alkaluman na masu zaman Jarun din guda 81,710 guda 53,790, suna zaman jirin a yanke masu hukunci ne.

Bugu da kari, wannan adadain, ya karu daga 47,610 a 2017, inda karuwar kai kaso 12.98.

Wannan adadin dai, matukar abin damuwa ce, ga dukkan wani mai tunani, musamman duba da cewa, sama da kaso .65 na ‘yan Jarun din, sun kasance wadanda ba a same su, da aikata wani laifi ba.

Hakan ya nuna cewa, ba wai ana tafiyar da gidan gyran hali bane, waje ne kawai na da ake fama da talauci.

Bisa alkaluman da NBS ta fitar a 2024, an samu karin  tabarbarewar tsarin kan  yawan masu zaman gidan da ya kamata a ajiye.

Misali, a 2026, daga jimlar yawan masu zaman gidajen, sun kai  guda 176,536 94,614 da ke zaman jiran a yanke masu hukunci.

Wadanda suka aikata sata sun kai su 55,722, inda wannan adadin, ya nuna shi ne, yafi yawa daga cikin wannaan laifukan, da aka aikata.

Laifin fashi da makamai, ya kai yawan 10,090, laifun cin hanci da rashawa, sun kai guda 27, da laifin masu aikata laifun kutse a yanar gizo, inda laifun fasakauri, suka kai  118.

Idan har kasar, ba ta tashi tsaye wajen magance cin hanci da rashawa a tsakanin wasu manyan kasar ba, to bangaren na shari’a zai ci gaba da kamawa da kuma hukunta wasu marasa karfi, da ke yin sata, domin abinda za su ci.

Misali, mutumin da ya saci wayar tafi da gidanka, shi ma an sanya shi a cikin jeren masu lafi guda 55,722.

Amma dan siyasar da ya yi sama da fadi da miliyoyin kudaden da aka tsara domin gina Asibitoci da Makarantu, an sanya su jeren masu laifin cin hanci su guda 27.

Hakan dai, na ci gaba da kara rashin yardar da ‘yan kasar ke da ita, daga banragen doka da oda.

Hakazalika, adadin masu zaman gidajen su 53,790 d ba a yanke wa hukunci ba, na ci gaba da jin jiki, saboda yadda tsarin, ya gaza daidaita komai.

Wasu da daga cikinsu da dama, sun shafe shekaru, sun a zaman jiran a yanke masu hukunci, amma kotuna, na ci gaba da daga sauraron kararsu, saboda kawai, wani ra’ayi, na kashin kai, inda ko dai, dansanda mai gabatar da kara, yaki halartar zaman kotun, ko kuma ayiwa Alkali canjin wajen aiki, ko kuma kudin karar, ya bace.

Kazalika, akwai kuma wasu da suka gaza cika sharuddan samun bayar da su, beli, inda wasun da yawa kuma, ba su masaniyar hakikain laifin da suka aikata.

A bangare daya kuma, lauyoyi masu tsayawa wadanda ayyuka sun yi masu dimbin yawa.

Mu a wannan Jaridar, abinda Nijeriya ke bukata, ya wuce batun gina gidajen gyran hali.

Bugu da kari, abinda kasar ke bukata shi ne, yanke hukunci kan lokaci da kuma bayar da beli.

Matukar ba a kawo karshen wannan kalubalen ba, matsalar za ta kawai, ci gaba da karuwa ne, a kasar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *