An kai hari fadar Basarake an yi garkuwa Sarki da ɗansa
[ad_1]
Rahotanni na bayyana cewa, an yi garkuwa da Basarake Aniwo na 1 na al’ummar Aafin, gundumar Ile-Ire, a Ƙaramar hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara, Oba Simeon Olaonipekun da ɗaya daga cikin ’ya’yansa Olaolu.
Olaolu wanda a halin yanzu yake yi wa ƙasa hidima NYSC, a wani mummunan hari da suka kai a fadar.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a daren Laraba, a jajibirin sabuwar shekara, inda aka yi zargin wasu gungun ’yan bindiga kimanin 8 ne suka kutsa cikin fadar da misalin karfe 8 na dare, inda suka yi ta harbe-harbe da neman ganin sarkin da matarsa.
Wata majiyar iyalan da ke cikin fadar a lokacin da harin ya auku ya shaida wa jaridar The PUNCH ta wayar tarho a ranar Alhamis cewa, an firgita ne yayin da maharan suka buɗe wuta.
“Da misalin ƙarfe 8 na dare na ga wasu motsin baƙi a waje, nan take na sanar da waɗanda ke ciki, muka fara kulle dukkan ƙofofin tare da kashe fitulun ciki, amma da suka fahimci abin da muke yi, sai suka fara harbe-harbe kai tsaye. Cewar majiyar.
Majiyar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, ’yan bindigar sun tilasta hanyar shiga fadar ne ta hanyar fasa ƙofar da bindigogi inda suka buƙaci ganin Basaraken Oba.
“Su kusan takwas ne saboda na gansu daga inda na ɓuya, sun yi amfani da bindigu suka fasa ƙofar, suka shiga suka nemi Basaraken, sai ya fito.
“Suna neman matarsa ma, amma harsashi ya same ta a hannu, a lokacin da suke yunƙurin shiga,” in ji majiyar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link