Tinubu Ya Ƙudiri Aniyar Magance Ƙalubalen Nijeriya – Sanata Danbaba Dambuwa
[ad_1]
Daga Rabi’u Ali Indabawa
Sanata mai wakiltar Mazaɓar Sakkwato ta Kudu a Majalisar Dattawa ta 8 da ta 9, Ibrahim Abdullahi Danbaba Dambuwa (DBB), ya bayyana cewa, shugaba Bola Tinubu ya kudiri aniyar magance dukkan kalubalen da kasar nan ke ciki. Sanata Danbaba ya bayyana haka a cikin sakonsa na taya ‘yan Nijeriya murnar shiga sabuwar shekarar 2026, tare da addu’ar fatan alheri.
“Yayin da muka shiga sabuwar shekarar 2026, ina mika gaisuwa ta musamman da fatan alheri ga daukacin al’ummar Jihar Sakkwato da kuma ‘yan Nijeriya baki daya. Allah ya sanya wannan shekara ta zama ta sabuwar fata, zaman lafiya da ci gaba mai dorewa ga kasarmu mai albarka,” in ji shi.
- ’Yansanda Sun Kama Mutane 2 Kan Sace Matan Aure A Kaduna
- Da Ɗumi-Ɗumi: Chelsea Ta Raba Gari Da Koci Enzo Maresca
Ya ce, “Ina amfani da wannan dama domin taya ‘yan Nijeriya murna da kuma mika gaisuwa ta musamman ga Mai Girma Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, jagora mai jarumta da kishin kasa wanda jajircewarsa wajen sauya fasalin Nijeriya ke kara zaburar da miliyoyin ‘yan kasa.
“Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta dauki matakai masu karfi na gyara, duk da kalubale da suka biyo baya, kuma suna gina tubalin sabuwar Njjeriya mai karfi da dogaro da kanta.
“Kokarinka a matsayin Shugaban Kasa na farfado da tattalin arziki, karfafa hukumomi da inganta tsaro abin yabo ne. Saboda haka, ina kira ga yan Nijeriya da su ci gaba da nuna hakuri da goyon baya domin ganin wadannan manufofi sun haifar da gagarumin sakamako a nan gaba,” in ji shi.
Ya c igaba da cewa; “Ga Mai Girma Gwamnan Jihar Sakkwato, Dr. Ahmed Aliyu (PhD, FCNA, ACIT), ina mika godiya ta musamman bisa jajircewarka wajen ci gaban jiharmu.
Ayyukanka a fannonin gine gine, kiwon lafiya, ilimi da tsaro sun nuna hangen nesan ka na gina Sakkwato daya, mai ci gaba da hadin kai. Jagorancinka ya dawo da kuzari a harkokin mulki tare da farfado da fatan al’umma.
Haka zalika, ina mika girmamawa da yabo ga jagoran siyasar mu, Mai Girma Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, Sarkin Yamman Sakkwato, wanda hikimarsa, shawarwari da jajircewarsa ga jam’iyyar APC suka taka muhimmiyar rawa wajen gina siyasar Jihar Sakkwato da Arewa gaba daya. Goyon bayansa da jagorancinsa na ci gaba da zama ginshiki ga wannan gwamnati da kuma haske ga sabbin shugabanni masu tasowa.”
Mu shiga wannan sabuwar shekara da sabuwar a zama da niyyar ci gaba da goyon bayan shugabanninmu, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Ahmed Aliyu yayin da suke kokarin cika alkawurran da suka dauka.
Mu zama jakadun zaman lafiya, wakilan ci gaba da kuma gwarazan hadin kai a cikin al’ummominmu.
[ad_2]
Source link